An gurfanar da fasto mai shekaru 60 bisa laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 13 fyade

0
94

Wata Kotun Majistare ta Aba ta Kudu ta tasa keyar wani Fasto mai suna Chukwuemeka Orji dan shekara 60 a gidan yari a ranar Talata bisa zargin yi wa wata karamar yarinya fyade.

Limamin cocin Assemblies of God na fuskantar tuhuma guda daya na yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade da ta wuce.

Wanda aka yi wa fyaden (an sakaya sunanta) ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya san ta a mace a lokuta da dama.

Ta ce bayan yi mata fyade karo na uku, ta shaida wa matarsa, Mercy, wadda rahotanni suka ce ta tunkare shi kan zargin.

Wacce aka yi wa fyaden ta yi ikirarin cewa faston ya musanta zargin a gaban matarsa.

Ta ce Orji, ya ci gaba da yi mata fyade tare da yi mata barazanar cewa zai  mayar da ita wurin iyayenta da ke kauyen Ugwunagbo idan ta fallasa shi.

Ta ce wannan barazanar ya hana ta gaya wa iyayenta da ke ibada a wani reshe na cocin abin da ta shiga.

Ta ci gaba da cewa, a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, bayan matar Orji ta tafi kasuwa, ya nemi ya yi lalata da ita, amma ta ki amincewa da cewa tana jinin haila.

Ta ce Orji, ya tilasta mata ta tsotse shi lamarin da ta bayyana a matsayin tashin hankali a gare ta.

Ta ce saboda ba za ta iya gamsar da shi ba, sai ya umarce ta da ta yanke ciyawa da ta tsiro a cikin gidansu “a matsayin hukunci”.

Ta ce bayan aikata laifin 15 ga watan Yuni ta je makaranta tana kuka.

“A lokacin da nake kuka ne mai makarantarmu ya tambaye ni dalilin kuka na gaya masa gaskiya.

Ta ce a lokacin ne aka gayyaci ‘yan sanda kan lamarin.

Orji ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi bayan an karanta masa tuhumar da ake masa, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Bayan gabatar da nasa labarin, Alkalin kotun, Misis Jane Young-Daniel, ta kira matar Orji ta wayar salula, inda ta tambaye ta ko tana sane da zargin da ake yi wa mijinta.

Bayanai sun bayyana cewa da farko Mercy ta musanta cewa tana sane da wannan zargi amma daga baya ta amince cewa ta ji hakan kuma ta fuskanci mijin nata, wanda ta ce ya musanta zargin.

Mai gabatar da kara na ‘yan sanda, Misis Mary Udoji, ya bukaci kotu da kada ta bada belin wanda ake kara domin hana shi ci gaba da lalata da yarinyar.

Young-Daniel ya ba da umarnin a mayar da yarinyar ga iyayenta nan take bayan an gaya mata cewa tun a hannun ‘yan sanda take.

Ya kuma ba da umarnin a tsare Orji a gidan gyaran hali na Aba.

Ta dage sauraron karar zuwa ranakun 6 da 18 ga watan Yuli domin sauraren karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here