Hukumar EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Benue Ortom bayan shafe sa’o’i 10 a komar su

0
126

Bayan shafe sama da sa’o’i 10 a ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC,  a Makurdi, tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, 

Gwamnan ya samu rahoton da safiyar ranar Talata da misalin karfe 10 na safe a ofishin shiyya na hukumar sakamakon gayyatar da ofishin ya yi masa.

An bayyana cewa hukumar ta gayyaci tsohon Gwamnan ne domin ya amsa zarge zargen da aka yi masa kan shugabancinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar.

Bayan ya kwashe tsawon yini a Hukumar, an ga yadda ake fitar da tsohon Gwamnan daga ofishin EFCC a cikin wata mota kirar SUV, da misalin karfe 7:55 na yamma, tare da rakiyar wasu abokai da abokan arziki da suka yi sansani a wani otal da ke kusa da da hukumar.

Ko da yake ba a iya samun tsohon gwamnan don jin ta bakinsa ba, amma sanarwar da aka fitar jim kadan kafin a sake shi da yammacin ranar Talata, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Terver Akase ya nuna cewa ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama shi ba.

Akase a cikin sanarwar ya bayyana cewa “ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke yada labaran karya ba, a yau ne tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya ziyarci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC domin karrama goron gayyatar hukumar.

“Ba a kama Cif Ortom ba kuma ba a tsare shi a hedikwatar EFCC da ke Makurdi.

“Tsohon Gwamnan ya sha nanata cewa a shirye yake ya amsa tambayoyi daga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa saboda ba shi da wani abin boyewa game da shugabancinsa na jihar Benue.”

A halin da ake ciki babu wani jami’in EFCC da ya bayar da bayanin kan ziyarar da tsohon Gwamna ya kai ofishin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here