Mun kwato filaye na tiriliyan din Nairori sakamakon rusau – Gwamnatin Kano

0
154

Gwamnatin jihar Kano ta kwato filaye da darajarsu ta kai tiriliyan nairori tun bayan da ta fara aikin rusau a wasu wurare a jihar. 

Sakataren gwamnatin jihar Dr Baffa Bichi ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels TV a cikin shirin  Siyasa a Yau.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wasu gine-gine a otal din Daula, filin Idi na Kano, kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu.

Ta zargi gwamnatin da ta shude da yin sama da fadi da dukiyar jihar, amma tsohon gwamnan, Abdullahi Umar Gnaduje, ya bayyana zargin a matsayin maras tushe.

Bichi ya ce, “Wani yana ikirarin cewa an ruguza gine-gine na Naira biliyan 129.

“Mun kwato kadarori (filaye) na jihar Kano na tiriliyan Naira da gwamnatin da ta gabata ta karkatar ga kansu da iyalansu. Filin Idi kadai ya kai tiriliyan din nairori. A kimar da a kai masa”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here