PSG na daf da nada Enrique sabon kociyanta

0
107

Paris St-Germain ta kusan sanar da nada Luis Enrique a matakin sabon kociyanta.

Har yanzu PSG ba ta tabbatar da raba gari da Christophe Galtier ba, amma dai ana hasashen cewar ya gama horar da kungiyar, bayan kammala kakar da ta wuce.

Galtier, mai shekara 56, ya maye gurbin Mauricio Pochettino a Yulin 2022, amma ya kasa taka rawar da kungiyar ke bukata.

Ana ta alakanta Luis Enrique da kungiyoyi da yawa, bayan da ya bar horar da tawagar Sifaniya, wadda ba ta yi abin kirki ba a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

PSG ta koma batun Enrique, mai shekara 53, bayan da ta kasa cimma yarjejeniya da tsohon kocin Bayern Munich, Julian Nagelsmann.

Luis Enrique ya taka rawar gani a lokacin da ya taka leda a Barcelona daga baya ya zama kociyan kungiyar ta Camp Nou tsakanin 2014 zuwa 2017.

PSG na son bunkasa kungiyar, sannan za ta yi watsi da batun daukar fitattun ‘yan wasa, wadanda suka kasa ci mata Champions League, kofin da ta ke bukata.

Galtier ya fara jan ragamar PSG da kwarin gwiwa a kakar da ta wuce, wanda ba a doke su ba wasa 22 da tazarar maki biyar tsakaninta da ta biyu a League 1 daga nan aka je gasar kofin duniya.

Daga baya kungiyar ta sha kashi a wasa tara, bayan da aka kammala gasar kofin duniya aka koma wasanni, inda Bayern Munich ta fitar da PSG a Champions League a zagayen ‘yan 16.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here