Tsananin zafi ya yi ajalin kusan mutum 100

0
112

Akalla mutum 96 ne aka tabbatar da mutuwarsu a sassan kasar India a cikin ’yan kwanakin da suka gabata saboda tsananin zafin da ake fama da shi.

Tuni dai mahukuntan kasar suka dukufa kokarin tantace ko tsananin zafin da ake fuskanta a kasar na da alaka da wannan asarar rayukan.

A arewacin jihar Uttar Pradesh da gabashin Bihar, jimillar mutum 96 ne suka mutu, a yayin da hukumar kula da yanayi ta kasar ke gargadin cewa za a fuskanaci tsananin zafi a sauran yankunan Arewa maso Gabashin kasar.

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar dai ta sanar da cewa yanayin zafi ya kai tsakanin 42 zuwa 45 a ma’aunin Celsius a jihohi 5 a karshen makon da ya gabata.

Hukumar ta kuma shawarci mutane su kasance a cikin gidajensu a yayin da yanayin ke kara zafafa.

Gwamnatin kasar ta ce tana gudanar da bincike a game da musabbabin mutuwar mutane a cikin kwanaki 3 na makon da ya gabata a gundumar Ballia ta jihar Uttar Pradesh, mai nisan kilomita 970 daga Kudu maso Gabashin birnin New Delhi.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan da kantoman gundumar ta Ballia, Ravindra Kumar, ya bayyan a shakkun ko mace-macen da suka auku sakamako ne na yanayin tsanannin zafi da ake fuskanta.

A wasu sassan kasar, lamarin dai ya fi shafar mutane ne masu yawan shekaru. ()

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here