Wata mace ta haihu a cikin jirgin saman Legas zuwa Amsterdam

0
170

Wata mace mai juna biyu ta haihu bayan naƙuda ta zo mata ba zato ba tsammani a cikin jirgin KLM da ke kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam daga Legas.

Lamarin dai ya tilasta wa jirgin yin saukar gaggawa a ƙasar Sifaniya.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne cikin daren Litinin, inda daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin KLM mai lamba 588, ƙirar Boeing 777, ta fara nakuda.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kai matar wadda ba a bayyana sunanta ba gaban jirgin, inda ta haifi ‘ya mace.

Bayan nan ne sai jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Barcelona inda ma’aikatan lafiyan da aka kira suke tsaye suna jira

An ce uwa da ‘yar duka suna cikin ƙoshin lafiya.

Mai magana da yawun kamfanin sufurin jiragen sama na KLM, Marjan Rozemeijer, a ranar Talata ta ce, “Zan iya tabbatar da cewa an haifi jaririyar a cikin jirgin KLM mai lamba KL 588 da ke kan hanyar zuwa Amsterdam a ƙasar Netherlands daga Legas.

Saboda dalilai na tsare sirrin mutum ba zan iya yin wani ƙarin bayani game da haihuwar ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here