Za a kai ɗan shugaban Amurka kotu a kan mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba

0
90

Ana sa rai Hunter Biden ɗan gidan Shugaban Amurka Joe Biden zai amsa laifi a kan aikata ba daidai ba game da biyan haraji kuma zai amsa cewa ya mallaki wata bindiga ba bisa ƙa’ida ba lokacin da yake shaye-shayen ƙwaya.

Matakin na zuwa ne bayan wani bincike na tsawon shekara biyar.

Babban lauyan Amurka a Delaware ne ya gabatar da takardun bahasin da ke nuna wannan yarjejeniya da aka cimma.

Ana sa ran Hunter zai amince cewa an yi masa magani saboda matsalar shan ƙwayar da ya yi fama da ita, kuma hukumomi sun sa ido a kansa.

Mai yiwuwa ne sharuɗɗan yarjejeniyar za su ba shi damar kuɓuta daga ɗauri a gidan yari.

A kan takarda, zai iya fuskantar hukuncin ɗauri mafi tsanani na tsawon shekara ɗaya a gidan yari a kan kowacce daga cikin tuhume-tuhumen da harajin da aka yi masa da kuma ɗaurin shekara goma a gidan yari a kan tuhumar mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, in ji wata sanarwa daga ma’aikatar shari’a.

Akwai buƙatar alƙalin da ke sauraron shari’ar kuma zai yanke hukunci, sai ya amince da yarjejeniyar da aka cimma.

Ba a fayyace ƙarara ba ranar da Hunter Biden zai bayyana a kotu don amsa laifi a kan tuhume-tuhumen haraji.

Zai amsa laifi kan mallakar bindiga a wani ɓangare na “yarjejeniyar madadin shari’a” wadda ita daban ce da bahasin da ya amsa. lauyan Mista Hunter ya faɗa a cikin wata sanarwa.

“Na san cewa Hunter ya yi imani abu ne mai muhimmanci ya ɗauki alhakin waɗannan kura-kurai da ya yi a lokacin gada-gada da jarabar shaye-shaye na rayuwarsa,” Mista Clark ya ƙara da cewa.

“Yana zuba ido don ganin ya ci gaba da sake gina rayuwa da kuma fuskantar gaba.”

Hunter Biden, ɗan shekara 53, ya taɓa aiki a matsayin lauya a shekarun baya da kuma jami’in kamun ƙafa ciki har da a ƙasashen waje kamar China da Ukraine.

An kore shi daga Rundunar Sojin Ruwan Amurka a 2014 bayan gwaji ya nuna yana ta’ammali da kokino.

Yarjejeniyar amsa laifin ta kawo ƙarshen wani bincike da ma’aikatar shari’ar Amurka ta shafe tsawon lokaci tana gudanarwa a kan ko Hunter Biden ya ba da cikakken rahoton kuɗin shigarsa da kuma ko ya ba da bayanan ƙarya a takardun da ya yi amfani da su wajen sayen wata bindiga a 2018.

Tuhume-tuhumen harajin na da alaƙa da gazawar sa wajen biyan harajin sama da $100,000 a shekara ta 2017 da kuma a shekara ta 2018

Tuhuma a kan bindigar ta faro ne kan wani batu na mallakar bindigar a shekara ta 2018 lokacin da yake ta’ammali da ƙwaya.

A cikin wani littafi da aka wallafa a shekara ta 2021, magajin Biden ɗin ya amsa cewa ya taɓa kasancewa mai jarabar shan ƙwayar kokino.

Sai dai an ba da rahoton ya ce “a’a” a kan fom ɗin gwamnatin tarayya da aka tambaye shi idan ya taɓa kasancewa “mai sha, ko jarabtuwa da, tabar wiwi ko kuma wata ƙwayar sanya nutsuwa, a-ji-garau, ko hodar iblis da duk wani nau’in kayan maye”.

Yarjejeniyar ta zo ne daidai lokacin da wasu ‘yan majalisa da ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Republican suka zargi Joe Biden da mayar da ma’aikatar shari’a “makamin” yaƙar abokan adawa.

Hunter Biden ya daɗe yana fuskantar bin diddigi daga masu ra’ayin gurguzu, waɗanda suka yi zargin cewa harkokinsa a ƙasashen waje na nuna wani samfurin cin hanci da rashawa.

Labarin yarjejeniyar amsa laifin ya gamu da gagarumar suka cikin sauri daga Donald Trump da kuma ayarin yaƙin neman zaɓensa, har ma da manyan ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here