Ali Maɗagwal ya sake barin Kwankwasiyya

0
166

Fitaccen mai wasan barkwanci a Kannywood  Ali ‘Artwork’ Maɗagwal ya sake komawa APC bayan ya kasa samun shiga a gwamnatin NNPP mai mulki a jihar Kano.

Ali Maɗagwal ya wallafa hotonsa da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC Nasriru Yusuf Gawuna a shafinsa na Facebook sannan ya rubuta “Gawuna is coming. Kano First.”

Shi dai Maɗagwal ya shahara ne a matsayin magoyin bayan siyasar Kwankwasiyya ta Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai lokacin zaɓen 2023 ya koma jam’iyyar APC musamman ma gidan ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, A.A. Zaura.

A nan ne ya kwancewa Kwankwaso zane a kasuwa, inda ya ce babu wani amfani da ya samu a tafiyar saboda babu ƙaruwa.

“Babu yadda za a yi in shekara 10 ina tafiyar da ko kobo ba a ɗauka a ban.” In ji Maɗagwal.

Amma bayan da Kwankwasiyya ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Kano sai ga Maɗagwal ya koma ɗan ma’abban sabon gwamna Abba Kabir Yusuf.

Duk da haka, haƙarsa ba ta cimma ruwa ba domin kuwa ya kasa samun hanyar da zai kurɗa ya samu shiga a Kwankwasiyyar.

Tun bayan zaɓe har zuwa rantsuwa ya na ta gwagwarmayar neman samun karɓuwa a Kwankwasiyya.

Da ya ga hakan ba ta samu ba sai ya fara tattara kayansa ta hanyar sukar  shirin gwamnatin na rushe gine-ginen da ta ce an yi su ne ba bisa ƙa’ida ba.

Kawo yanzu dai Maɗagwal ya tsallake ya koma APC inda ya cigaba da tallan Gawuna da Zaura a shafukansa na sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here