Dani Alves na fuskantar daurin shekaru 12 kan laifin fyade

0
95

Tsohon dan wasan baya na Barcelona, Dani Alves, na iya fuskantar daurin shekaru 12 a gidan yari, bisa zarginsa da fyade a wani gidan rawa na kasar Spain.

Ana sa ran za a gudanar da shari’ar kan zargin tsakanin watan Oktoba ko Nuwamba mai zuwa.

Tsare Alves

Tun a ranar 20 ga watan Janairu ake tsare da Alves, bayan da wata yarinya ‘yar shekaru 23 ta yi zargin ya yi mata fyade a wani gidan rawa.

Alves ya musanta zarge-zargen, amma an ki amincewa da bukatarsa na neman bada belinsa, kuma ya ci gaba da kasancewa a tsare a gidan yarin Brians 2 dake Katalonia.

Zai iya fuskantar daurin shekaru 12 a gidan yari idan aka tabbatar da laifin akansa.

Hana shi beli

Kotun koli a Barcelona ta yi watsi da bukatar Alves na baya-bayan nan na neman a sake shi daga gidan yari.

A cewar Marca, akwai fargabar cewa Alves na iya tserewa daga kasar idan aka sake shi, watakila zuwa kasarsa ta Brazil, wadda ba ta mika ‘yan kasarta idan kotun wata kasa ta yi bukatan haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here