‘Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin kuɗin wuta da kashi 40%

0
175

Da alama dai ‘yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin kuɗin lantarki na fiye da kashi 40% nan da wasu kwanaki.

Matakin zai tabbata ne matuƙar sabuwar dokar lantarki ta fara aiki.

Ana tsammanin cewa dokar za ta bai wa shugaban Najeriya damar janye tallafin kusan naira biliyan hamsin da gwamanti ke kashewa a ɓangaren samarwa da raba wutar lantarki.

Haka zalika, masu ruwa da tsaki a ɓangaren lantarki za su yi wani zama da hukumar kula da rarraba wutar lantarki a ranar 1 ga watan Yuli don ɗaukar matsaya a kai.

Su dai masu ruwa da tsaki a ɓangaren, na kallon matakin a matsayin wani cigaba, bisa la’akari da yadda tsarin samar da lantarki yake a sauran ƙasashen duniya.

Ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin kula da harkar lantarki a majalisar wakilan Najeriya da ta gabata, Injiniya Sani Bala Tsanyawa, a wata hira da BBC ya ce ba shi da tabbacin yadda ƙarin zai kasance.

Sai dai, a cewarsa bisa yadda abubuwan suke musamman yadda kamfanonin lantarki ke ta ƙorafi, ba mamaki a ƙara kuɗin da kusan kashi 40%.

Me dokar ta ce?

Ɗan majalisar wakilan ya ce dokar ta tanadi bai wa jihohi da ɗaiɗaikun mutane damar samar da lantarki na ƙashin kansu, da kuma sarrafa ta, da rarraba ta.

Ya ce manufar ita ce bai wa masu hannu da shuni damar shiga harkar, tun da ta bayyana cewa gwamnati ba za ta iya bai wa jama’ar ƙasar baki daya wuta ba.

”Akwai manyan masu kuɗi da kamfanoni da ke son su yi hakan, to amma babu doka, don haka wannan mataki a yanzu zai sa wutar ta wadata, sannan ya kasance an yi abin bisa tsari” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: ”Da ma ita wuta(r lantarki) a yanzu an riga an wuce zamanin samun ta a kyauta, ba aba ce da samun ta ke da sauƙi ko araha ba”.

Ana kukan targaɗe…

A baya-bayan nan ne, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kara farashin litar man fetur bayan janye tallafinsa, lamarin da ya sa ‘yan ƙasar da dama guna-guni.

Ƙarin farashin muhimman harkokin rayuwa kamar man fetur da lantarki a Najeriya na haifar da tashin farashin komai da ake amfani da shi, domin ko da aka kara kudin man fetur a baya-bayan nan an samu tashin farashin kusan komai da ninkin baninkin.

Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin ‘yan kwadago da gwamnati kan mafi karancin albashi na Naira dubu dari biyu da ‘yan kwadagon ke ganin an amince da shi sakamakon karin man da aka yi.

Sai kuma ga wannan batu na karin kudin wuta da ya taso a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here