An kashe Mutane 201 a Filato cikin watanni 5

0
106


Akalla mutane 201 ne aka bada rahoton sun mutu a cikin watanni biyar a hare hare 27 da aka kai kananan hukumomi 7 na jihar Filato, kamar yadda jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa ta ruwaito.

Kashe kashen sun auku ne daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa ranar 20 ga watan Yunin wannan shekarar da muke ciki.

Kananan hukumomin da wannan lamari  ya shafa sune: Riyom, Bokkos, Jos  ta Kudu, Jos ta Gabas, Barkin Ladi, Bassa da Mangu.

An tattara wadannan allkalumman ne daga kashe-kashen da  aka samu labarin su a jihar ne, kuma ana hasashen za a samu karuwar mamata.

Mazauna jihar da masu sharhi sun bayyana takaici a game da kashe kashen da ke aukuwa kwanan nan a jihar, inda suka ja hankali a kan makamancinsa a shekarar 2001, wanda aka kai shekaru sama da 10 ana yi, lamarin da ya lakume rayuka da kadarori da suka kai  bilyoyin nairori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here