Komammen shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya sha alwashin bincikar tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje game da bidiyon da aka gan shi ya na cusa kuɗi a aljihunsa.
Jaridar Daily Nigerian ce dai ta yaɗa bidiyoyin da ta ce Dr. Abdullahi Ganduje ne yake karɓar kuɗin cin hanci daga wurin ƴan kwangila.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta zargin tun a lokacin.
Amma a hirar da ya yi da tashar talabijin ta Trust TV, Muhuyi Rimin Gado, wanda Ganduje ya cire shi bayan sun samu saɓani, kuma gwamnan yanzu Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bisa umarnin kotu, yace binciken ya zama wajibi.
“Lokacin da ina ofis mun fara bincike amma akwai tarnaƙi kasancewar gwamna mai ci ya na da kariyar sharia.
“Sai dai yanzu tun da ya sauka, kariya ta sauka, hukuma za ta yi abin da ya dace,” in ji Muhuyi Rimin Gado.