DSS ta fara gayyatar makusantan dakataccen shugaban EFCC, Bawa bayan binciken ofishinsa da gidansa

0
207

Jami’an hukumar ‘yansandan tsaron cikin gida ta farin kaya (DSS) sun gudanar da bincike a gida da ofishin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) wanda aka dakatar, Abdulrasheed Bawa a Abuja.

Jaridar PUNCH ta samu labarin cewa, rundunar ‘yansandan ta sirri, ta kuma gayyaci makusantan Bawa a hukumar ta EFCC domin amsa tambayoyi kan zargin almundahana, almubazzaranci da kuma karkatar da kudaden kadarorin da EFCC ta sayar.

Sai dai a ranar Laraba da aka tuntubi kakakin hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya, kan yadda binciken ke gudana ya ce, “Babu wani sharhi a yanzun”

Bawa, wanda a halin yanzu yake tsare a hannun hukumar DSS “Yellow House,” Abuja, ana tuhumarsa da laifin cin amanar ofishinsa a matsayin shugaban EFCC.

Jaridar PUNCH ta tattaro cewa an gudanar da bincike a gidansa na Gwarinpa da ke Abuja a ranar Asabar, a gaban iyalansa.

Wata majiya mai tushe, ta bayyana cewa wata rundunar hukumar DSS din kuma ta yi bincike ofishin Bawa a ranar Asabar din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here