Faɗan manya: Masu kamfanin Twitter da Facebook za su dambace

0
167

Manyan attajiran da suka mallaki kamfanonin  Twitter, Facebook da Instagram sun shirya gwada ƙwanji domin fid-da-raini tsakaninsu.

Mai Twitter, Elon Musk ne ya fara tsokana inda ya wallafa cewa a shirye su yi ‘faɗan keji’ da mai Facebook da Instagram, Mark Zuckerberg.

Shi faɗan keji dambe ne da ake kulle mutane a cikin keji su bai wa hammata iska har sai wanda aka kayar ya sallama.

Bayan da Zuckerberg ya ga saƙon Musk sai ya mai da martanin “turo min inda zamu haɗu.”

Nan take kuwa Musk ya amsa da cewa “Vegas Octagon”.

Wannan ne dai wurin da ake yin kokawar UFC ta cikin keji a birnin Las Vegas, dake jihar Nevada, Amurka.

Mr Musk mai shekaru 52 ya yi ƙaurin suna kan rashin motsa jiki yayin da Mr Zuckerberg mai shekaru 39 ƙwararre ne a dabarun faɗan ƴan China musamman ma samfurin Jiu-jitsu.

Yanzu haka dai masu bibiyar mutanen biyu a kafafen sada zumunta su na nan sun fara haɗa hotuna kan yadda suke ganin faɗan zai kasance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here