Biranen bakin teku na fuskantar barazanar ambaliya a Afrika – Rahoto

0
148

Wani rahoton kwarraru ya yi hasashen karuwar tumbatsar ruwan teku da rabin mita nan da shekarar 2050 kana yakai akalla karuwar mita 2 nan da shekarar 2100, lamarin da zai yi gagarumar illa ga biranen da ke gab da teku musamman a yammacin Afrika.

Galibin manyan biranen Afrika da ke gab da ruwa da suka kunshi Lagos a Najeriya da Abidjan a Cote d’Ivore baya ga Accra a Ghana za su zama ‘yan gaba gaba da za su gamu da illar da wannan matsala ta tumbatsar Teku za ta haifar wadda za ta kai ambaliyar ruwa da gurbacewar iska.

Rahoton kwararrun ya bayyana cewa yanzu haka wannan matsala ta tumbatsar teku tun gabanin ta kai ga tsananta a 2030 ta na haifarwa nahiyar asarar dala biliyan 4 duk shekara wanda zai iya rubanyawa zuwa dala biliyan 10 nan da 2100.

Kasashen nahiyar ta Afrika musamman wadanda ke gab da gabar teku na ganin bala’o’in da dumama ko kuma sauyin yanayi ke haifarwa kama daga ambaliyar ruwa zaftarwar laka ko kuma mahaukaciya guguwa a lokutan kakkarfan ruwan sama.

Rahoton ya bayyana cewa lura da yadda wadannan birane na gab da teku ke samar da kashi kashi 56 na karfin tattalin arzikin nahiyar Afrika a ma’aunin GDP kamar yadda rahoton Bankin Duniya na 2020 ke bayyanawa, hakan na nuna bukatar da ake da ita na daukar mataki don bayar da kariya daga ibtila’in da ke tunkaro su.

Biranen da wannan matsala ke tunkarosu sun kunshi kusan dukkanin yankunan da ke da kasa da tazarar kilomita 300 da tekun Atlanta ciki kuwa har da Accra da Keta da kuma Takoradi a Ghana kana Saint-Louis da Dakar da Ziguinchor a Senegal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here