Da ikon Allah babu bacci ko daga kafa sai na shawo kan matsalar tsaro – Gwamnan Zamfara

0
128

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ayyana cewa ba zai yi bacci ko daga kafa ba da ikon Allah sai ya shawo kan matsalar tsaro a Zamfara. Gwamnan ya sha wannan alwashi ne yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC a wannan makon, in ya yi bayanai masu muhimmanci da suka hada da tarin matsalolin da ya tarar da su a jihar da suka shafi ilimi, Ruwan sha da kuma rashin biyan albashin ma’aikatan jihar.

Ga dai yadda hirar ta kasance kamar yadda RABI’U ALI INDABAWA ya rubuto mana:

Daga lokacin da Allah ya baka kujerar Gwamnan Zamfara ya ka samu kanka a matsayin gwamna?
Alhamdu lillahi, mun amshi wannan mulki, kuma kamar yadda nake zato abubuwan da muka samu sun ma fi tunanina, tun da muka amshi mulkin nan mun samu asusun Zamfara babu kudi, kusan asusu daya na gani watakil in ce kamar akwai miliyan uku ko miliyan hudu.

…Na Naira ko na Dala?
Na Naira, yau jihar nan wata uku ba a biya albashi ba kuma har yanzu a kai ake. Sannan yau idan ka duba duk ma’aikatun da ke Jihar Zamfara an yanke musu wuta ana bin su bashi, bashi na miliyoyi dari-dari. Yau idan ka duba duk wata ma’aikata tun daga ma’aikatar shari’a ko jami’an tsaro yau ba biya kudadensu na yau da kullum na tafiyar da harkokinsu ba fiye da wata uku. Da na tattauna da alkalai sun gaya min cewa wata uku ko kwabo ba a basu ba, saboda haka yanzu ma ba a iya zama a yi shari’a don ko takardar da za su yi rubutu yanzu ba su da ita. Jami’an tsaro na zauna da su yau wata uku ‘yankudaden da ake ba su na yau da kullum da za su shiga nan su shiga can babu su. kai motocin ma da suke amfani da su yanzu wallahi ba su da tayoyi ballantana a ce maka kudin mai da makamantansu. Yau ‘yan makaranta daliban Zamfara Saifuros jiya an yi min waya cewa an kore su, daliban Zamfara, a Indiya, an yi min waya an kore su. yau da muke maganar nan wani dalibi na Jihar Zamfara bai rubuta NECO ba bai rubuta WAEC ba saboda ana bin gwamnati fiye da Naira biliyan 1.6. yau idan ka je gidanmu na Kaduna na gwamnati kotu ta kulle shi ana bin mu kudi. Jiya-jiyan nan a Abuja gidajenmu na gwamnati kotu ta zo ta sa a kulle su ana bin mu kudi.

Kafin ka samu wannan nasara ta zama gwamna ka taba tunanin wannan matsalar
Na yi tunanin wadansu daga cikinsu kamar yadda na ce, amma da na zo sai na ga cewa abin ma ya wuce misali.

Ka yi maganar an bar kusan miliyan uku zuwa hudu, amma gwamnatin APC da ta tafi ta fito tana cewa ta bar kudi kusan biliyan ashirin a asusun gwamnatin Zamfara har da wasu daloli kusan miliyan uku haka.
Na ji wannan, sannan na ce don Allah don Annabi ina so a zo a nuna mana shi a wane asusu ne aka ajiye wannan kudi. Kuma sun san cewa suna da wannan kudin a she keta ta hana a biya ma’aikata kudadensu, keta ce ta hana a ba da kudaden da za a sayo sinadaren da za a kai hukumar samar da ruwa, keta ta hana a biya ‘yan makaranta kudadensu, keta ce ta hana a biya jami’an tsaro kudadensu, keta ce ta hana duk wadannan koyu da muke fama da su da makamantansu, don Allah ina roko a nuna min wane asusu ne kuma a nuna wa duniya bayanan cewa ga biliyan ashirin da gwamnati ta bari.

Yanzu me ka fara da shi?
Na farko maganar ruwa, kusan wata hudu ke nan babu ruwa a cikin garin Gusau, to Alhamdu lillahi wannan sati na zagaya na je gida na ga irin matsalolin da suke fama da su, na farko da ba su da wuta saboda an yanke wutarsu fiye da wata hudu, na biyu babu ‘yan sinadaran da ake sawa wanda da shi a ke tura ruwa al’umma su yi amfani da shi, sai da na je ciwo bashi aka sayo wadannan sinadarai aka zo sa. Sannan da ikon Allah kuma na samu wasu bayin Allah Indiyoyi da suka zo wasu na’urori wanda na roke su suka bamu kyauta. Na’urorin nan in za a saye su za a kashe miliyan 200.

Kana maganar ba kudi gashi har ka ciyo bashi ka fara tunkarar matsalar ruwa, mutanen nan na Zamfara ma’aikata ga su kusan watansu uku ko hudu ba albashi, kana ganin bai da muhimmanci a samu su rage zafi musamman a wannan lokacin na janye tallafin mai?
Abin da zan iya tabbatar wa ma’aikatan Jihar Zamfara da ikon Allah za mu yi kokari mu biya albashin su kafin Sallah, duk yanda zan yi duk hanyar da zan bi in biya albashi in Allah ya yard azan biya su.

Na wata nawa?
To na farko zan ga nawa ne bashin da za a iya bani, idan zan iya biya fiye da wata daya zan biya in kuma ba zan iya ba, zan biya wanda na san wannan hakkina ne a wannan wata in basu kafin in ga wace hanya ce zan bi in samo wasu kudaden don in tabbatar da cewa wannan bashi da suke bin gwamnati na dauke shi daga kan gwamnati.

Yanzu baru mu je kan tsaro, bayan hawanka kusan kila ka shaida ganin kalubalen da ke gabanka, musamman an kai hare-hare a Maradun, an kai a yankin Maru, an kai kuma Jangebe har kashe wani likita, a Bakura ma an yi.
Kwarai da gaske

To yanzu ya ka ji kuma me za ka yi a kai?
Abu ne mara dadi, duk wani shugaba ba wanda zai so ya je cewa yau an zo an kashe wani mutumin jiharsa, na ji zafin wannan abu kuma na jajanta wa wannan al’umma, muna nan muna bakin kokarinmu na tabbatar da cewa an kawo tsaro a Jihar Zamfara. Na farko cikin satin nan da ni da sauran gwamnonin Arewa da Yamma mun zauna da shugaban kasa kuma mun gaya masa irin matsalolin da muke fuskanta ta wajen tsaro, wanda ya tabbatar mana da cewa yana sane da wadannan matsaloli kuma shima yana bakin kokari ya ga cewa an shawo kan wannan matsala. Bayan mun gama wannan tattaunawa, na je na zauna da shi shugaban sojojin na Nijeriya baki daya wato ‘Chief Of Army Staff’ kenan na kara tabbatar masa da irin matsalolin da muke fuskanta na rashin tsaro ya bani tabbacin cewa a shirye suke su taimaka wajen kawo tsaro a Zamfara.

To batun hanyoyi da ka yi magana akwai wasu hanyoyi, akwai batun sulhu ciki?
Wato abubuwan suna da yawa, abu nd sa za a tattauna a gani kan cewa shin maganar sulhu ta yaya za a yi in ma sulhun za a yi, ba zan iya gaya maka sauran abubuwan ba saboda abu ne na maganar tsaro amma dai in mun cimma iyaka na san su da kansu jami’an tsaron za su fito su yi wa al’umma bayani kan irin matakan da aka dauka.

Wane alkawari za ka yi ma ‘yan Zamfaran nan kan tsaron nan kila a cikin kwanakinka dari?
Abin da zan iya cewa maganar tsaro ita ce kan gaba a wannan mulki nawa, ba zan yi bacci b aba kuma zan daga kafa ba sai na tabbatar da cewa da ikon Allah mun ciyo kan matsalara tsaro.

To mu je batun ilimi ka ce yara ba su rubuta jarrabawa ba kuma an gaya maka a Saifuros an kori daliban Zamfara, batun ilimin nan kusan zamfara ita ce baya, me ka shirya yi a gaggauce wanda kila zai iya tunkarar wannan batu.?
Na farko abin gaggawa shi ne zan zauna da ‘yan NECO da ‘yan WAEC don mu shiga cikin wata yarjejeniya yadda zan iya biyan wadannan kudade da suke bin gwamnati, wanda idan mun biya dalibanmu za su iya komawa makaranta in lokacin jarrabawa ya yi kuma za su iya zauna wa wannan jarrabawa yadda za su amshi takardar shaidarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here