EFCC ta kama ‘yan damfarar intanet da dama a Enugu

0
133

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta ce jami’anta sun kama mutane da dama da ake zargi da yin damfara ta intanet a Enugu da ke kudu maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafukanta na soshiyal midiya ranar Juma’a ta ce jami’anta da ke Enugu sun kama “mutum 33 da ake zargi da yin damfara ta intanet a wani samame” da suka kai musu.

Ta kara da cewa an kama mutanen ne ranar 20 ga watan Yuni.

Mutanen da aka kama su ne:

Micheal Ogobodo

Michael Elijah

Sopuluchukwu Michael

Michael Joshua

Ogu Jerry

Ebuka Okafor

Ehinyameh Eromosele

Emeka Okongwu

Jane Ogwunga

Okpara Chidera

Emmanuel Abah

David Okwo

Chidozie Okpara

Ngene Samuel

Onuh Kelvin Uchechukwu

Ebuka Kalu Bewell

Oba Stanley Ikechukwu

Kalu Chukwudalu

Ifeanyi Jeff Ukwuoma

Paschal Ugwuanyi

Chukwuma Peter

Ukwuoma Nmasi Joseph

Obiozor Franklin

Chimaobi Kelvin Azubuike

Okafor Damian

Kulugh Simio

Okafor Ifeanyi Gabriel

Ugochukwu Nnabife

Godwin Ifeanyi

Henry Chima

Arinze Ogu

Emmanuel Peter

Godwin Miracle

Hukumar ta EFCC ta ce ta kwato abubuwa da dama daga hannunsu da suka hada da motocin alfarma hudu, wayoyin salula 49, konfuta bakwai, na’urar ajiye bayanan komfuta wato Flash drive da ya da kuma fasfo guda daya.

Ta kara da cewa mutanen da ake zargi sun yi magana kan abubuwan da ake tuhumarsu da aikatawa kua za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Damfara a intanet wani batu ne da ke neman zama ruwan dare a Nijeriya inda galibin masu yinsa suke sace makudan kudade daga hannun jama’a, ciki har da ‘yan kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here