NLC taki amincewa da karin kudin lantarki

0
153

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ƙi amincewa da shirin da ake yi na ƙara kuɗin wutar lantarki da kaso 40% nan da 1 ga Yulin 2023.

A sanarwar da ya fitar a Abuja, Kwamared Ajaero ya ce shirin na nuna halin ko-in-kula da rayuwar talakawan Najeriya.

Hukumar kula da farashin lantarki ta ƙasa (NERC) ce ta amince da ƙarin kuɗin saboda tashin farashin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.

Sai dai shugaban na NLC ya buƙaci gwamnati ta hana wannan ƙarin kuɗin wutar.

A cewarsa “dole ne ayi la’akari da adadin wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke kawowa da kuma ƙarfin aljihun masu amfani da lantarki wurin biyan kuɗin”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here