Najeriya da Ghana sun kulla yarjejeniyar dakile laifukan kan iyaka

0
174

Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na Najeriya da Ghana, EFCC da EOCO sun sanya hannu kan wata yarjejeniyata yadda za su hada kai wajen magance laifukan da suka shafi rashawa a kan iyakokin kasashen, musamman ma wadanda ake yi a intanet.

A wata sanar da EFCC ta fitar ta ce, da yake jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a hedikwatar hukumar a Abuja, shugabanta na rikon kwarya, Abdulkarim Chukkol ya bayyana yarjejeniyar da cewa wata kololuwa ce ta jerin ayyukan hukumomin kasashen biyu da aka gabatar a kwanakin da suka gabata.

“Na yi imanin wannan yarjejeniya ba a takarda kawai za ta tsaya ba, za mu tabbatar mun aiwatar da ita, kuma aiwatarwar za ta fara ne daga yau,” ya ce.

Chukkol ya kuma bayyana cewa yarjejeniyar za ta yi aiki ne a matsayin gargadi ga masu aikata laifuka a kasashen biyu, cewa abubuwa sun sauya.

“Ina fatan idan kun koma kasarku, wasu abubuwan da kuka gani, masu kyawu, to za ku aiwatar da su a can.

“Kuma idan akwai abin da kuke son tuntubar mu a kai, ko neman taimakonmu, musamman a kan batun kwace kadarori kan batun zambar intanet da gurfanar da mutum, to a shirye muke mu hada gwiwa da ku.

“Ba mu da wani zabi saboda laifuka sun zama na wata kasar na shiga wata, don haka ina ganin wannan taron namu na yau zai zama gargadi ne cewa aikata laifi baya haifar da alheri.

“Duk inda kake, za mu je mu kamo ka a kowane lokaci,” ya kara da cewa.

Me jami’an Ghana suka ce?

A nata bangaren, shugabar tawagar ta hukumar yaki da cin hanci ta Ghana, Maame YaaTiwaa Addo-Daquah ta ce ta ji dadin irin tarbar da ak yi musu, da shirye-shiryen da aka gabatar da kuma makalolin da jami’an EFCC suka gabatar.

Jami’an EOCO suna ziyarar aiki ne ta kwana biyar a Nijaeriya, wacce ta kawo karshe a ranar Juma’a 23 ga watan Yunin 2023 :Hoto: EFCC

Ta bai wa hukumar tabbacin cewa kokarinta ba zai tashi a banza ba. “Zan iya cewa EFCC za ta yi alfahari da mu idan ta ji cewa hukumarmu ta EOCO ta sauya daga yadda take gudanar da al’amuranta.

“Ina da tabbacin kokarinku ba zai tashi a banza ba. Za mu aiatwar da wannnan yarjejeniyar, don idan ba mu yi ba tamkar mun bata wa kowa lokaci ne. Sannan ina mai tabbatar muku za mu tuntube ku a duk abin da ya shiga mana duhu,” a cewarta.

Jami’an EOCO suna ziyarar aiki ne ta kwana biyar a Nijaeriya, wacce ta kawo karshe a ranar Juma’a 23 ga watan Yunin 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here