Saran maciji ya kashe kwamandan ISWAP a jahar Borno

0
140

Daya daga cikin kwamandojin kungiyar ISWAP ya mutu a jahar Borno, sanadiyar sarar da maciji ya yi masa.

A cewar Zagazola Makama wani kwararre wajen yaki da ta’addanci a yankin tabkin Chadi, ya ce kwamandan na ISWAP da ake kira da Kiriku, ya mutu ne a ranar Juma’a kwanaki uku bayan sarar macijin a maboyar su a yankin karamar hukumar Damboa.

Ya ce mutuwar ta Kiriku na da nasaba da rashin kulawa tun bayan sarar da maciji ya yi masa.

Kafin mutuwar sa, Kiriku ya jagoranci kai hare-hare a yankin Jiddari da ke Chiralia, yankin da ke zaman matattarar Boko Haram da kuma ISWAP.

Haka nan ya jagoranci kai harin kwanton bauna kan jami’an sojojin da ke aiki a karkashin rundunar Operation Hadin Kai a jahar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here