Aikin Hajjin bana ya samu halartar mafi yawan Mahajjata a tarihi

0
133

A karon farko tun bayan kullen cutar Corona, mahajjata kimanin miliyan biyu da rabi za su gudanar da aikin hajji a bana, kamar yadda wata majiya daga hukumar kulada aikin Hajji da Umara ta kasar Saudiya ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP.

Haka nan aikin hajjin na bana shine ya samu halartar mahajjata mafi yawa tun bayan da kasar ta sanya dokar hana mata zuwa aikin hajji ba tare da muharrami ba a shekarar 2021.

A shekarar 2020 da aka samu bullar cutar corona a duniya, kimanin mahajjata dubu 10 ne ka dai suka gudanar da aikin Hajji, sai dai a shekarar 2021 adadin ya karu zuwa dubu 59, ya yinda a shekarar da ta gabata kimanin mahajjata miliyan daya ne suka gudanar da aikin Hajji.

Wani dan kasuwa a kasar da ke kasuwancin samar da gidajen saukar Alhazai Samir Al-Zafni, ya ce dukkanin gidajensa a Makkah da Madina a cike su ke.

Sakamakon cinkoso da kuma tsananin zafin da ake fama da shi a kasar ta Saudiya, hukumominta sun ce an tanadi jami’an bada agajin gaggawa dubu 32 da za su kula da mahajjata a masallacin Harami, sabida matsalar tsananin zafin da ake ganin zai iya kaiwa digiri 45 na ma’aunin Celsius, wanda kuma ka iya sanya mahajjata galabaita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here