Tanadin da aka yi wa alhazan Najeriya da ke shirin Misha’ir daga birnin Makkah

0
149

A daren wannan Lahadi ne alhazai za su fara tafiya Misha’ir daga birnin Makkah, wato kebantattun wuraren ibada da suka hada da Mina, Arafa da Muzdalifa da kuma wajen jifan Shaidan, domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Kwamishina mai kula da harkokin ma’aikata da kudi a hukumar alhazai ta Najeriya, wato NAHCON, Nura Hassan Yakasai, ya shaidawa BBC cewa daga bangarensu a bana suna fatan komai zai tafi daidai ba tare da samun cunkoso ba.

“In sha Allahu yau lahadi alhazan Najeriya za su fara fita zuwa Mina, inda za su yi sansani har zuwa wayewar Talata”.

Yadda aikin zai kasance

A cewar kwamishinan za a fara aikin kwashe alhazai ‘yan Najeriya a ranar Lahadi daddare har zuwa daren Litinin.

Ya ce fatansu shi ne kafin wannan dare an kwashe dukannin ‘yan Najeriya zuwa Mina domin shirin gudanar da hawan Arafa a ranar Talata.

‘Yan Najeriya dubu 75 suka je kasa mai tsarki ta hanyar hukumar kula da alhazai ta kasa, yayin da alhazai dubu 20 ne suka shigo ta jirgin yawo.

Wannan ne ya sa adadin ‘yan Najeriya da za su yi aikin hajji bana ya kai dubu 95.

Hukumar ta Nahcon ta kuma ce sun shirya tsaf game da aikin jigilar alhazai ‘yan Najeriya da kaucewa duk wasu kura-kurai.

“Akwai motocin da za a kai a kowane gidan alhazai, za su yi ta jigila har sai sun kwashe dukkanin alhazan jihohi.

“Ma’aikatanmu sun je sun duba duka tantuna da ya kamata a ce alhazan Najeriya sun zauna a ciki watau (Mina da filin Arafa)”.

Mahukutan Najeriya sun ce an dauki matakin ganin ba za a samu cunkuso a cikin tantuna ba kuma duk abubuwan da ya kamata a sa a cikin tantuna kamar karpet da katifofi da AC duk suna ciki.

Domin kauce ma turmutsin da ya faru a shekarar 2015 inda mutane da dama suka rasa rayukansu, mahukuntan Saudiyya sun fitar da wani tsari na rage yawan cunkuson mutane da ke zuwa jifan shaidan.

Tsari ya nemi kasashe ko jihohi su rika tafiya da wani kaso na mutanen da za su yi jifa.

‘Ana saran kafa tarihi’

Ana gudanar da aikin na bana a karon farko, tun bayan shekara ta 2019 ba tare da dokokin korona ba.

Ana saran kafa tarihi, inda maniyatta sama da miliyan biyu daga kasashen duniya 160 za su sauke farali a bana.

Dubun-dubattan maniyatta na ta gudanar da dawafi da sauran ayyuka na ibada a masallacin harami.

Ana dai bukatar kowanne musulmi mai hali ya gudanar da aikin hajji akalla sau guda a rayuwarsa, abin da ya sa mutane da dama ke tanadin kudi ko adashin gata domin sauke wannan farali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here