Ana caccakar Obama a Indiya kan kalamansa na kare haƙƙin Musulmai

0
162

Shugabannin jam’iyya mai mulki a Indiya sun soki kalaman tsohon shugaban Amurka Barack Obama game da take haƙƙin Musulmai a ƙasar.

Mista Obama ya faɗa a wata hira a makon da ya gabata cewa Indiya ka iya “fara ɓalɓalcewa” idan har ba ta kare haƙƙin marasa rinjaye.

Yana amsa tambaya ne game da yadda Shugaban Amurka Joe Biden ya kamata ya yi mu’amala da ƙasashe “‘yan dimokuraɗiyya amma masu tsaurin ra’ayi”.

Firaministan Indiya Narendra Modi na ziyarar aiki a Amurka a daidai lokacin.

Yayin ziyarar tasa, an yi masa maraba a Fadar White House cikin shagali, da liyafar abincin dare da kuma saka hannu kan wasu yarjejeniyoyi.

Kazalika Modi ya yi wa taron haɗin-gwiwar majalisun Amurka jawabi.

Kafofin yaɗa labarai a Indiya sun yaɗa hirar da Obama ya yi da wakiliyar CNN Christian Amanpour, wadda aka saki kafin ya gudanar da jawabi a majalisar.

Ta tambayi Obama: “Ta yaya shugaban ƙasa ya kamata ya yi mu’amala da shugabanni wajen ambaton sunansu ko kuma hulɗa da su?”

Mista Obama ya ce “abu ne mai sarƙaƙiya”, kafin ya bayyana irin halin da ya shiga wajen hulɗa da ƙawayen Amurka da “ba sa bin salon dimokuraɗiyya da ya dace” amma kuma dole ƙasar ta ci gaba da ƙawance da su saboda wasu dalilai.

Ya ƙara da cewa “zai yi kyau” shugaban Amurka, idan zai yiwu, ya ƙalubalanci “lamurran da ba su dace ba” a bayyane ko a ɓoye.

Shugaba Biden da Firaiminsta Narendra Modi a lokacin ganawarsu
Bayanan hoto,Shugaba Biden da Firaiminsta Narendra Modi a lokacin ganawarsu

Ya ƙara da cewa “Idan shugaban ƙasa ya haɗu da firaiminista Modi, ya kamata ya kawo masa batun kare haƙƙin Musulmai a ƙasar ta Indiya, wadda mafi yawan al’ummarta mabiya addinin Hindu ne.”

“Idan da a ce zan tattauna da Modi a yanzu, wanda mun san juna sosai, ɗaya daga cikin abin da zan faɗa masa shi ne idan ba ka kare haƙƙin ƙabilu marasa rinjaye a Indiya ba, to akwai yiwuwar cewa nan gaba ƙasar za ta fara darewa.”

Mista Obama dai ya kasance yana ɗasawa da Modi a lokacin mulkinsa.

Ministar kuɗi ta Indiya, Nirmala Sitharaman, wadda ita ma ƴar jam’iyyar BJP ce mai mulki, ta shaida wa manema labaru cewa ta “kaɗu” da kalaman tsohon shugaban na Amurka Barack Obama.

Ta ce: “A daidai lokacin da Mista Modi ke bayani kan lamurran Indiya a Amurka – wani tsohon shugaban ƙasar shi kuma yana surutu kan Musulman Indiya.

Sitharaman ta ƙara da cewa Amurka a lokacin Obama ta jefa bama-bamai a ƙasashen Musulmai, kamar Syria da Yemen.

Shi kuwa ministan tsaro Rajnath Singh ya mayar da martani inda ya ce Indiya ba ta taɓa tsangwamar wasu mutune saboda addininsu ba.

Ya ci gaba da cewa “Masu iƙirarin kare haƙƙin tsiraru su tsaya su yi tunani kan ƙasashen musulmai nawa ne suka kai wa hari.”

Gwamnatin Amurka da kuma shi Obama ɗin ba su ce komai ba kan jerin martanin na manyan ƴan siyasan ƙasar ta Indiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here