Babbar Sallah: Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun Sallah, 28 da 29 ga watan Yuni

0
193

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni, 2023 a matsayin ranakun hutu don gudanar da bikin Sallah Babba ta bana.

Wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade, ya bayyana a ranar Litinin a Abuja.

Sanarwar ta bukaci Jama’a da su gudanar da shagulgulan biki lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here