Halittun da ‘ba sa mutuwa’ da masana kimiyya ke mamaki a kai

0
184

Daga tatsuniyoyi zuwa labaran adabi na kimiya, buƙatunmu na ƙuruciya an adana su a rubuce.

Amma akwai wasu halittu da suka saɓa tunani ko saboda shekaru – kuma suna nan a zahiri.

Za su iya zama haka ko muna tunanin tun asalin halittarsu ba za su mutu ba. Wannan yana nufin, sai idan an kashe su ta hanyar farauta, ko wata cuta ko sauyi na muhallinsu, amma za su iya rayuwa har abada.

Masana kimiyya sun yi ƙoƙarin gano sirrin waɗannan halittu masu ban mamaki don ganin ko za su iya taimakawa wajen gano alaƙar tsarinmu na tsufa.

Ga uku daga cikin waɗannan halittun na ban mamaki.

Tsutsar Planarian

Tun ƙarni na 19 aka fahimci wata nau’in tsutsa ta planarian kan farfaɗo da kanta idan ta rabu biyu.

Amma wannan halittar ta zama ruwan dare a 2012, lokacin da Jami’ar Nottingham ta wallafa wani bincike kan yiyuwar rashin mutuwarta.

Wannan nau’in tsutsa, ana samun ta a sassan duniya kuma akwai nau’ukanta 12 a Birtaniya.

Nau’in tsutsar yana da karfin ƙwayoyin halitta da ba ya da iyaka na sake farfaɗowa.

Tsutsar  Planarian
Bayanan hoto,Tsutsar Planarian za ta iya raba kanta biyu ta sake gina kanta

Akwai nau’i biyu na irin wannan tsutsar: Wasu suna hayayyafa ne ta hanyar jima’i wasu kuma ta hanyar rabuwa biyu.

Masana kimiya na Jami’ar Nottingham sun yi nazari kan duka nau’ukan biyu kuma sun gano cewa waɗanda ke rabuwa biyu suna iya farfaɗowa.

A wasu lokuta na rayuwarmu, kwayoyin halittarmu na DNA kamar yawancin dabbobi sukan kai maƙura na rarrabuwa kuma jikinmu zai fara lalacewa.

Tsutsar planarian kuma a ɗaya ɓangaren sukan samu ƙaruwar sinadaran jiki da ake kira enzyme da ke kare kwayoyinsu daga tsufa, wanda masana kimiya suka yi imanin cewa ba za su iya mutuwa ba.

Tsutsar Hydra

Wannan wata halittar ruwa ce da ke da ƙamboli a baki.

Hydra na cikin cikin halittun da masanin kimiya na Netherland, Van Leeuwenhoek, wanda ya samar da na’urar gani ta microscope da gilashi ɗaya mai girma ya yi nazari a kai.

Ba da daɗewa ba binciken masanin kimiya na Switzerland Abraham Trembley kan tutsar hydra da ƙarfin farfaɗowarta ya samar da sabon zamani na fannin ilimin nazarin halittu.

Haka kuma, tsutsotsin hydra suna da ƙarfin iya farfaɗo da sassan jikinsu.

Kuma ƙarfin yiyuwar kasancewar waɗanda ba su mutuwa ya dogara ne da ƙwayoyin halittarsu.

Masanan da suka yi nazari tsawon shekaru kan nau’in hydra sun kasa gano wata alama ta tsufa a tattare da su.

Tsutsar Hydra
Bayanan hoto,Tsutsar Hydra

A 2018, masu bincike daga UC Davis sun yi wani hasashe cewa tsutsar hydra za su iya zama halittar da ba ta mutuwa saboda irin karfin sarrafa ƙwayoyin halittar da ake kira ‘transposon, wani nau’in kwayar halittar da ke tsalle.

Lokacin da muna da ƙuriciya jikinmu kan iya sarrafa waɗannan ƙwayoyin halittar, amma yayin da muke tsufa za mu fuskanci ƙalubale.

Kifin Torritophis dohrnii

Wannan kifin wanda a kimiyyance ake kira Torritophis dohrnii na rayuwa ne a ruwa.

A 1880 aka fara gano shi a Bahar Rum, kuma ana iya samunsa a wasu wurare da dama saboda ratsawar manyan jirage a ruwa.

Halitta ce ƙarama da ke cin ƙwaƙwayan kifi da wasu ƙananan halittin ruwa.

Kifi
Bayanan hoto,Kifin da ba ya mutuwa yana iya rikidewa ya koma matashi

Wani abin mamaki game da wannan nau’in kifin shi ne yadda yake iya saita yanayin rayuwarsa.

Idan ya shiga damuwa yakan rikiɗe ya koma rayuwarsa ta baya.

Kuma ba ya ga haka. Lokacin da kifin ya koma matakin rayuwarsa na baya, yana kuma haifar da ƙarin kwayoyin halitta – don haka, a zahiri, yayin da yake zama ƙarami yana ƙara sabunta kansa.

An fara wallafa wannan maƙalar a watan Yunin 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here