Ba za mu yi tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindiga ba – Gwamnatin Zamfara

0
136

Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Najeriya ta ce, ba za ta taba shiga wata tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindigar da ke addabar jihar.

A yayin zantawa da manema labarai a birnin Gusau, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Nakwada ya ce, wannan sabuwar gwamnatin ba ta da niyar zaman tattaunawa da wani shugaban ‘yan bindiga ko kuma wakilinsu da sunan cimma yarjejeniyar zaman lafiya wadda a can bayan ba ta yi aiki ba.

Nakwada ya sanar cewa, gwamnatin a shirye take ta fatattaki ‘yan bindigar tare da murkushe su da masu daukar nauyinsu.

Sakataren ya kuma ce, gwamnatin za ta yi aiki tukuru tare da hadin guiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa, an tunkari ‘yan bindigar a maboyarsu.

Har ila yau jami’in ya kara da cewa, gwamnatin da ta shude karkashin jagorancin tsohon gwamna Mohammed Bello Matawalle ta barnatar da biliyoyin naira kan wasu ayyuka da ya ce, ba su da amfani kai-tsaye wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

A cewarsa, sabuwar gwamnatinsu za ta yi duk mai yiwuwa domin kwato wasu kadarorin jihar kamar motoci da tsohuwar  gwamnatin ta sayo ta kuma rarraba wa makusantanta.

Jihar Zamfara na cikin jerin jihohin arewacin Najeriya da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke garkuwa da jama’a suna karbar kudin fansa, yayin da a wasu tarin lokuta suke yin kisa babu kakkautawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here