Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta dakatar da albashin ma’aikata sama da 10,000

0
157

Gwamnanatin Kano ta bayyana dalilin da ya sa ta dakatar da albashin sama da ma’aikata 10,000 da gwamnatin baya ta dauka aiki.

Gwamnatin ta yi zargin cewa an dauki ma’aikatan aiki ba bisa ka’ida ba kuma an dauke su a lokacin da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ke daf da mika mulki.

A wata tattaunawa da manema labarai a Kano, Akanta Janar na jihar Abdulkadir Abdusalam ya ce ma’aikatan an dauke su ne ba bisa tsari ba da alfarma kuma wasu ba su cancanta ba.

“Mai girma gwamna ya umarta a dakatar da wadannan ma’aikata wadanda sun kai kusan dubu goma da dari bakwai da wani abu zuwa da dari takwas, ya ce a tsaida su ba za su karbi albashi a wannan watan ba sai an yi bincike na yadda aka yi aka dauke su aiki,” in ji Abdulkadir Abdulsalam.

“Akwai zargi na cewa wasu da yawa daga cikinsu takardunsu ba nasu bane na bogi ne, akwai zargi da yawa wasu ‘ya’yan shafaffu da mai ne wanda suna can wasu kasashe suna karatu, ba sa zuwa ko wurin aikin amma an dora su a sunan cewa ma’aikata ne su, ana karbar wadannan kudade ana ba su,” in ji shi.

Ya bayyana cewa a wannan dalilin ya sa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ba su umarni kan cewa a dakatar da albashinsu duka a yi bincike da kuma tantance wanda ake ganin ya dace da kuma wanda bai dace ba a tsayar da shi.

Akanta Janar din ya kuma yi karin haske kan batun wasu ma’aikatan kananan hukumomi da na hukumar SUBEB wadanda ya yi zargin an mayar da albashinsu a karkashin jiha saboda suna hanya inda ya ce an mayar da su manya-manyan makarantu saboda albashin makarantun na da tsoka.

“Mai girma gwamna ya umarta ya ce a dauke su a mayar da su ma’aikatun da suka fito, su ne kananan hukumomi, don haka a wannan watan albashinsu zai koma kan kananan hukumomi,” in ji shi.

Ya bayyana cewa duk da haka gwamnan ya ce cikin ma’akatan kananan hukumomin da aka mayar jiha za a bincika a tantance a ga wadanda suka cancanta su zauna a irin manyan makarantun domin a bar su.

Tun bayan karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, sabon gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya dauki matakai da dama wadanda wasu ke kallo a matsayin ramuwar gayya sai dai wasu kuma suna kallon matakan a matsayin yunkurin dawo da martabar Jihar Kano.

Daga cikin matakan farko da sabon gwamnan ya dauka akwai batun rusa kwamitin gudanarwa na hukumar jin dadin alhazai.

Haka kuma gwamnan ya rusa gine-ginen da gwamnatin ta ce an yi ba bisa ka’ida ba daga ciki har da katafaren shataletalen da tsohuwar gwamnatin jihar da gina.

Sai kuma aniyar da gwamnatin ta dauka na kwato filayen gwamnatin jihar da ake zargin an siyar ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here