Mahajjatan Najeriya sun yi wa kasa addu’o’i na musamman a filin Arfa

0
131
Alhazan Najeriya
Alhazan Najeriya

Manyan Malaman addinin Musulunci da mahajjata daga Najeriya sun gudanar da addu’o’i a ranar Arafah wacce ita ce ranar da ta fi kowacce muhimmanci a aikin Hajji, kan cigaba da daurewa da zaman lafiya, hadin kan kasa da bunkasar tattalin arzikin Najeriya.

Tawagar malamai a karkashin inuwar kwamitin malamai na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta gudanar da addu’o’i a wani zama na musamman da kwamitin tare da hadin guiwar shugabannin NAHCON suka shirya.

Malaman da mahajjatan sun yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara tare da rokon Allah da ya baiwa Shugaban kasa da tawagarsa hikima da karfin guiwa wajen tunkarar kalubale da dama da ke addabar Najeriya.

A cikin addu’o’insa na musamman a ranar,  Shahararren malami, makarancin Alkur’ani mai suna Sheik Ahmad Suleiman ya bayyana muhimmancin ranar, inda ya ce ranar Arafah ita ce mafi girman ranakun aikin hajji wacce ake amsa addu’o’i a aikinta.

Malaman addinin musulunci daga Najeriya da dama a wajen taron na musamman sun yi addu’ar zaman lafiya da hadin kan kasa da cigaban tattalin arzikin kasar.

A nasa jawabin, shugaban hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya taya daukacin alhazan Najeriya murnar samun damar halartar aikin hajjin bana musamman ranar Arafat mai dimbin daraja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here