Me ya sa jami’o’in Najeriya suka tsuga kuɗin makaranta?

0
178

Ana ci gaba da muhawara a Najeriya, tun bayan da Jami’ar Bayero ta Kano ta fitar da sabon jadawalin kuɗin rijistar makaranta ga ɗalibai, wanda ya zo da ƙarin kimanin kashi 200% a bana.

Ɗalibai da yawa sun firgita da ƙarin kuɗin makaranta ninki biyu tashi guda, har ma ana fargabar wasu na iya watsar da karatunsu na jami’a.

Hukumomin jami’ar Bayero dai sun ce sun yi ƙarin ne saboda gwamnatin tarayya ta cire tallafin da take bai wa jami’o’i a ƙasar.

A cewar Mallam Lamara Garba, jami’in hulɗa da jama’a na Jami’ar Bayero, sanin kowa ne gwamnati wadda ita ce ke tafiyar da harkokin jami’o’i ta ce ta cire hannunta a fannin ilmi mai zurfi kamar yadda ta cire a fannin man fetur.

Ya ce bisa la’akari da wannan yanayi, babu yadda za a yi jami’o’i su iya tafiyar da al’amuransu, ba tare da sun ƙara kuɗi ba.

Wata ɗaliba da ke karanta fannin kimiyyar kwamfiyuta a jami’ar ta shaida wa BBC cewa a bara kuɗin da suka biya don yin rijista a matsayin sabbin ɗalibai, bai fi N35,000 ba, amma a jadawalin da aka fitar bana, sabon ɗabili sai ya biya N110,000.

Lamara Garba ya yi iƙirarin cewa Bayero ce take karɓar kuɗin makaranta mafi ƙaranci a tsakanin duk jami’o’in Najeriya.

“Akwai jami’ar da na sani, 350,000 ta caza a waccan shekarar karatu, amma mu kuma a nan gaba ɗaya ƙarin da muka yi N95,000 ne zuwa N170,000 mafi yawa.”

Ya ce: “Idan ka yi la’akari…. Yanzu za ka ga misali a nan private secondary school, za ka ga yaro ana biyan N100,000 ko N200,000 ko N500,000 a term (wato a zango ɗaya) ba a shekara ba. Mu kuma wannan ƙari a shekara ne”.

Bayanai sun ce jami’o’in gwamnatin tarayya da dama a Najeriya ne suka yi ƙarin kuɗin rijistar, a cikinsu har da Jami’ar Tarayya ta Dutse.

Ƙarin dai ya shafi kusan dukkan wani fanni na karatun jami’ar kama daga masu karatun digiri na biyu da masu karatun difloma da masu neman digiri na uku.

Sanarwar da jami’ar ta fitar ta kuma yi nuni da hatta kuɗin makwancin ɗalibai ya ƙara kuɗi, inda kuɗin makwancin ya fara daga naira 37,000 har zuwa 300,000 ga mata ‘yan ƙasashen waje.

‘Na sha wahala kafin na biya’

Wani ɗalibin Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa su tun a farkon shekara, aka yi musu irin wannan ƙari. Ya ce lamarin ya sanya rayuwarsu da ta mahaifansu cikin ƙarin wahala.

“Ban taɓa shan wahala wajen biyan kuɗin makaranta kamar a wannan shekarar ba”.

Ya ce a baya lokacin da yake sabon ɗalibi N52,000 ya biya matsayin kuɗin makaranta.

Ya ce kamar yadda aka saba kamata ya yi a bana, ya biya N37,000 saboda mafi yawa ɗaliban da suke komawa suna biyan kuɗi, ƙasa da abin da suka biya a shekarar farko.

Sai dai, maimakon haka jami’arsu a bana, ta buƙaci ya N90,000.

Ibrahim ya ce wasu takwarorin ma suna biyan kuɗi fiye da haka. “Akwai waɗanda suke biyan kimanin 140,000”. Ya ce hukumomin makarantar ba su iya fayyace musu dalilin yin wannan ƙarin kuɗin makaranta ba.

Abokina ya daina zuwa jami’a

Ya ce mahaifinsa ya biya kuɗin makarantarsa na bana ne bayan ya sayar da amfanin gonar da ya noma.

Ɗalibin ya ce bai taɓa shan wahalar biyan kuɗin rijistar makaranta ba irin wannan shekara.

A cewarsa, akwai abokansa da yawa waɗanda ba su iya kammala biyan kuɗin makarantar ba. Ya ce hukumomin makarantar a bana ba su rufe lokacin kammala biyan rijista ba saɓanin a baya.

Haka zalika, ya shaida wa BBC cewa makarantar ta bar ƙofar biyan kuɗin a buɗe ta yadda ɗalibi na iya kai kafin alƙalami, sannan ya riƙa cika kuɗin a hankali kafin ƙarewar zangon karatu.

Duk da haka, ya ce akwai abokan karatunsa da ya sani waɗanda sun daina zuwa jami’ar tun bayan ɓullo da saboda tsarin biyan kuɗin.

“Akwai abokina da na sani tun da muka koma, ban gan shi ba. Ni ban sa shi a idona ba. Yau kusan watanmu uku da komawa. Tun da yanzu magana ma ake ta fara jarrabawa bayan sallar nan,” in ji Ibrahim.

Ya ce ya tuntuɓi abokin nasa a kan rashin komawar tasa, inda ya shaida masa cewa matsala ce ta rashin kuɗin makaranta.

Korafin ASUU da yajin aiki

A ƙarshen shekara ta 2022 ne, wasu jami’o’in Najeriya suka fitar sanarwar cewa daga zangon karatu na gaba, za su ƙara kuɗin makaranta.

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) tun a lokacin ta ce da ma ta san za a rina, saboda kuɗin gudanarwa da gwamnatin ƙasar ke bai wa jami’o’in, ba sa isa.

Da wuya a iya cewa ga lokacin da gwamnatin Najeriya ta cire tallafin ilimi mai zurfi a ƙasar.

Sai dai malaman jami’o’in ƙasar sun shafe tsawon wata takwas a shekara ta 2022, suna yajin aikin da ya kassara harkokin karatu jami’a.

Cikin muhimman buƙatu guda biyar da ASUU ta zayyana a matsayin dalilanta na shiga yajin aikin har da rashin wadataccen kuɗin gudanar da ayyuka don farfaɗo da jami’o’i.

Zulumi da damuwa tsakanin iyaye

A watan gobe ne za a koma zangon karatu na gaba a jami’ar Bayero, inda ake sa ran wannan ƙarin kuɗin makaranta zai fara aiki.

Wasu iyayen ɗalibai sun bayyana zulumi da damuwa a kan ƙarin, saboda a cewarsu da ma da ƙyar da jiɓin goshi suke iya biyan kuɗin makaranta a baya.

Ƙarin kuɗin makarantar dai ya zo ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa game da ƙarin tsadar rayuwa da hauhawar farashi bayan gwamnati ta janye tallafin man fetur a ƙarshen watan Mayu.

Bayan nan ne kuma, Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu a kan wata sabuwar dokar ba da bashi ga ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya kuɗin makaranta ba.

Babu masaniya zuwa yanzu a kan tasirin da irin wannan bashin karatu zai iya yi wajen rage wa ɗaliban manyan makarantu raɗaɗin ƙarin kuɗin makaranta.

Cire tallafin man fetur ya shafi fannonin rayuwa da dama ciki har da sufuri wanda ɗaliban ke amfani da shi wajen zuwa makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here