Abubuwan da ke sa wayar tarho zafi da yadda za’a magance su

0
150

Ka na zaune a waje da tsakar rana sai wayarka ta sanar da kai cewar ta yi zafi. 

Me za ka yi idan Tik Tok ya daina aiki, komawa hira da abokan aiki?

Matsanancin yanayin zafin da ake fuskanta a Burtaniya a yanzu, ba mutane kawai ya ke shafa ba hatta na`urorin lantarki su na ɗanɗanawa kuɗarsu.

To sai dai ba kamar Ƴan Adam ba, wayoyin hannu ba sa zufa. wanda abu ne mai kyau ga wadanda su ke rike da su amma kuma illa ne ga na`urorin.

Menene ya sa na`urorinmu su ke fama da zafi, ko akai abinda za mu iya yi?

Idan yanayin zafi ya tsananta aikin wayar hannu na raguwa.

Misalin yanayin da wayar hannu ta ke tsintar kai a ciki ya yi daidai da yadda mu ke takura kawunanmu wajen yin aiki cikin yanayin tsananin zafi.

“Dr Roz Wyatt-Millington malama ce a sashen koyar da kimiyyar ƙere-ƙeren lantarki a Jami`ar Leeds Beckett, ta ce na`urar da ta ke sarrafa bayyanai da aikewa da sakwanni a cikin wayar hannu ta na fidda zafi daidai da aikin da ta ke yi a lokaci”.

“Idan wayar ta dauki zafi, na`urar da ta ke daukar bayanai sai ta yi kokarin dakatar da zafi sakamakon haka kuma karfin batir zai ragu daga kashi 100 zuwa kasa da haka”.

Dakta Roz ta kara da cewar an kirkiri na`urori don su yi aiki kan matakin kuzari 35.

“Batur ne ya ke adana kuzarin da waya ta ke amfani da shi tsananin zafi ya na tasiri a aikin da waya za ta gudanar.

Wannan na nufin karfin batur zai yi saurin sauka idan akwai zafi saboda babu wani tanadi a cikin ƙwanson waya wanda zai sanyaya ta.

Dr Roz ta ce mu kan rashe hasken waya idan akwai hasken rana, wanda hakan na taimakawa kwarai.

Ƙonewar fuskar waya

Idan ka fahimci canji a fuskar wayar ka, zafi ne ya haifar da haka.

”Zafi ya na kara girman lalacewar wani bangare na tsohuwar waya, cewar Dr Roz”.

Ta kara da cewar kariyar da ake shimfidawa fuskar waya ta na kara zafi, kuma ba abu ne mai kyau ba a lokutan zafi.

Abin da za ka yi don sanyaya waya

  • A guji barin waya ta daɗe a caji.

“A lokacin yanayin zafi yayin da ku ke cajin baturi, zafi na karuwa a lokacin da na’urarku ta kasance a kan caji,” in ji Dr Roz.

  • Yadda za a ajiye waya

“Tsare waya daga hasken rana kai tsaye yana taimakawa kuma kar a bar ta cikin motar, a yi kokarin ajiye ta cikin inuwa gwargwadon iko.”

  • Rage mata nauyi

Wannan ya shafi cire mata kariya da kuma kashe duk manhajojin da ba a bukatar ayyukansu.

”Ta kara da cewar Idan ba ka amfani da GPS ka kashe shi. Saboda ƙarancin kayan da ku ke amfani da su a zahiri shi ne ƙarancin kuzarin batir”.

  • Amfani da takaitaccen kuzarin batur.

“A wasu lokuta a kashe waya gabadaya da zarar ta fara bayar da matsala, idan ta yi sanyi kadan sai a sake kunna ta.”

  • A guji sanya ta cikin na`urar sanyaya kaya
  • “Kunshe ta cikin jakar ƙanƙara ba shi da amfani.”

”Canjin zafin waya cikin gaggawa na iya haifar da matsala ga waya kuma Kanƙara na iya sanya ruwa ya makale a ciki..

”Dakta Roz ta ce wayoyin hannu su na da hanyoyin hana zafi ya lalata su a mummunan yanayi”.

BBCHAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here