Larabar nan take Sallar Layya, a sassan duniya daban-daban, bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji sun yi hawan Arafa a jiya Litinin.
Wani muhimmin abu yayin wadannan bukukuwa shi ne yin layya.
Bayan kammala sallar idi Musulmai masu hali za su yanka dabbobin da suka tanada don yin layya.
Biki ne da ake gudanarwa sau daya a shekara, inda jama’a ke dafa abinci, a ci a sha a yi hani’an, a kuma ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki.
Hatta wadanda ba su samu yin layya ba kan yi watanda, wato a hada kudi a sayi wata dabba don a yanka a raba.
Wasu kuwa da Ubangiji bai huwace masu ba sukan samu kyautar nama daga ‘yan uwa da abokan arziki don suma su gurje bakinsu, tun da kamar yadda Hausawa kan ce ne, Sallah biki daya rana.
Baya ga rabon naman da aka yanka na layya, akan kuma yi girki na gani na fada, a kuma yi ta aika wa ‘yan uwa da abokan arziki albarkacin wannan rana.
Ga yara kanana kuwa, a iya cewa wannan lokaci abu nasu ne maganin a kwabe su, duba da yadda a kan gwangwaje su da kwalliyar sabbin kaya na gani na fada.
Su kuma fita yawon salla gidajen ‘yan uwa da abokan arziki a ranakun farko- farko, daga bisani kuma a kai su gidajen wasa da sauran wuraren yawon bude ido don faranta masu.