Arsenal ta samu Timber, Hernandez zai tafi PSG

0
158

Dan bayan Netherlands Jurrien Timber, mai shekara 22, na shirin gabatar da kansa domin a yi masa gwajin lafiya a Arsenal bayan da Gunners din suka daidaita da Ajax a cinikinsa kan yuro miliyan 42. (De Telegraaf)

Har yanzu West Ham na jiran Arsenal ta gabatar mata tsarin da za ta bi wajen biyan fam miliyan 105 da ta sayi Declan Rice. (Sun)

Chelsea na neman a yi wata yarjejeniya tsakaninta da Brighton a kan cinikin Moises Caicedo, kasancewar tuni dan wasan na Ecuador ya cimma yarjejeniya ta baka da Blues din. (Fabrizio Romano)

Dan bayan Bayern Munich Lucas Hernandez, dan Faransa na dab da komawa Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta zabi dan wasan tsakiya na Celta Vigo Gabri Veiga, na Sifaniya a matsayin wanda ya fi dacewa ya maye gurbin Mason Mount wanda zai koma Man United. (Standard)

Aston Villa na duba yuwuwar aron Ferran Torres na Barcelona tare da zabin sayensa dindindin a kan yuro miliyan 25. (Mundo Deportivo)

Tsohon dan wasan Ingila Ruben Loftus-Cheek, yana Italiya domin kammala yarjejeniyar komawarsa AC Milan dindindin daga Chelsea, kuma Christian Pulisic, shi ne na gaba da Milan din za ta nemi saya daga Chelsean. (Standard)

Romelu Lukaku, ya sake watsi da tayi na biyu na tafiya kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya wadda za ta rika biyansa kusan fam miliyan 39 a shekara kasancewar yana son barin Chelsea ne kawai domin zama dindindin a Inter Milan. (Gazzetta dello Sport)

Juventus da Borussia Dortmund da Bayer Leverkusen na sha’awar matashin dan wasan Sheffield United na tawagar ‘yan kasa da shekara 20 ta Ingila Daniel Jebbison, mai shekara 19. (90min)

Manchester United da Chelsea na sha’awar mai tsaron ragar Aston Villa Argentina Emiliano Martinez. (Football Transfers)

Kociyan Manchester United Erik ten Hag ya dakile hanyar tafiyar mai tsaron ragar Ingila Tom Heaton, tafiya Luton Town, yayin da zaman David de Gea ba shi da tabbas a kungiyar. (Telegraph)

A yau Juma’a kwantiragin Wilfried Zaha zai kare da Crystal Palace, amma kuma ana sa ran dan wasan na Ivory Cosat ya kulla wani sabon wa’adin zama a kungiyar. (Mail)

West Ham na sha’awar dan bayan Arsenal Nuno Tavares, dan Portugal. (iNews)

Arsenal ta yi nasarar shawo kan matashin dan wasan Ingila Ethan Nwaneri, mai shekara 16, duk da sha’awar da Chelsea da Manchester City ke yi masa. (Telegraph)

Kociyan Roma Jose Mourinho na sa ran dibar ‘yan wasa biyu daga Leicester Kelechi Iheanacho, na Najeriya da kuma Patson Daka, dan Zambia. (Express)

Tson dan wasan Ingila na Leicester Jamie Vardy, ya yi watsi da tayin da kungiyar Khaleej ta Saudiyya ta yi masa. (Guardian)

Daniel Farke na dab da zama sabon kociyan Leeds United, inda kungiyar take sa ran samun Bajamushen kafin atisayen wasannin share fagen kaka a mako mai zuwa. (Mail)

Tsohon kociyan Crystal Palace Patrick Vieira, ya zama wanda ake sa ran zamamai horad da Strasbourg ta gasar Faransa. (Mail)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here