‘Buhari bai hana shugaba Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba’

0
115

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari bai hana Shugaba Bola Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba, a cewar kakakin tsohon shugaban kasar.

Wani sako da Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis daddare ya musanta cewa tsohon Shugaba Buhari yana katsalandan a binciken da sabuwar gwamnati ke son yi kan jami’an gwamnatin da ta gabata.

“Idan za a yarda da abin da aka ce a soshiyal midiya, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana bukatar mutumin da ya gaje shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu kada ya binciki tsoffin jami’an gwamnatinsa.

Wannan labarin karya ne, kada ma mu tattauna a kansa ko mu mayar da hankali a kansa. Wannan karya ce tsagwaronta”, a cewar sakon.

Wasu bayanai sun ce tsohon Shugaba Muhamadu Buhari ya gana da Shugaba Tinubu a birnin London domin rarrashinsa kada ya binciki tsoffin jami’an gwamnatin nasa.

Sai dai Mallam Garba ya karyata hakan, inda ya kara da cewa “babu kowa a dakin da suka gana sai su biyu kadai, don haka babu wanda ya isa ya bar da labarin abin da suka tattauna a kai.”

A cewarsa, tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari yana yin bakin kokarinsa wajen ganin bai janye hankalin sabuwar gwamnati ba.

“Ya zabi ya tafi Daura domin fatan samun nutsuwa amma da ya fahimci hakan ba mai yiwuwa ba ne, masu ziyara na zuwa wajensa ba dare ba rana, shi ya sa ya tafi wani wuri da ke nesa,” in ji sanarwar.

Tsohon shugaban yana fatan a bar shi ya huta kamar yadda ya kamata, kuma a bari gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu zarafin gudanar da ayyukanta don cika alkawuran da ta dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here