Harkar tsaron Najeriya ba abu ne mai sauki ba – Irabor

0
151
Lucky-Irabor
Lucky-Irabor

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor mai ritaya, ya ce samar da tsaro ga babbar ƙasa irin Najeriya ba abu ne mai sauki ba, amma kuma ya ce abu ne da za a iya cimmawa.

Janar Irabor ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar ranar Juma’a, a wajen taron karramawar barin aiki da aka shirya masa a barikin soji na Mogadishu Cantonment da Abuja babban birnin ƙasar.

Ya ce akwai jan aiki mai yawa a gaban sojojin ƙasar na bai wa ƙasar tsaron da take buƙata.

Ya kuma bayyana gamsuwarsa kan gudunmowar da ya bayar a aikin sojin ƙasar, yana mai cewa zai bar rundunar sojin ƙasar fiye da yadda ya same ta.

Tsohon babban hafsan tsaron ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasar su guji aikata abubuwan da ka iya zubar wa rundunar sojin ƙasar kima.

Yana mai cewa rundunar a shirye take domin kawo haɗin kai da zaman lafiya da kare rayukan ‘yan ƙasar.

Ya kuma yi fatan sabon babban hafsan tsaron zai ɗora a kan ciyar da rundunar sojin kasar gaba.

A shekarar 2021 ne tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa Irabor a matsayin babban hafsan tsaron ƙasar wanda ya maye gurbin Abayomi Olonisakin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here