Morocco ta yi wa jakadanta a Sweden kiranye saboda wulakanta Alkur’ani a kasar

0
121

Maroko ta umarci jakadanta a Sweden da ya janye aikinsa a kasar har zuwa wani lokaci, sakamakon yagawa da kuma kona Alkur’ani da wani mutum ya yi a wajen babban masallacin birnin Stockholm, a cewar kamfanin dillacin labarai na kasar.

Kazalika Ma’aikatar harkokin wajen Maroko ta umarci babban jami’an da ke huldar jakadancinta a Sweden ya koma Rabat da safiyar ranar Alhamis inda ta bayyana kakkausar sukar da masarautarta ta yi kan kona littafi mai tsari.

Da fari dai ‘yan sanda a Sweden ba su dauki mataki ba kan wulakanta Alkur’ani da wani mai tsattsauran ra’ayi ya yi, amma daga baya sun kaddamar da bincike na kalaman nuna kiyayya.

A rubutacciyar takardar da ta fitar ta bayar da izinin kona littafin mai tsari, rundunar ‘yan sandan Stockholm ta bayyana a ranar Laraba cewa “babu wani yanayi da ya tabbatar da yin hakan, a karkashin dokokin da ake da su, zai sa a yi watsi da wannan bukatar”.

Yayin da wannan lamari ke kara fusata al’umma, ‘yan sandan sun ce tuni suka fara gudanar da bincike kan kalaman nuna kyama kan mutumin, dan asalin kasar Iraki, kan kona Alkur’anin a gaban wani masallaci da ke gundumar Sodermalm a birnin Stockholm, a daidai lokacin da Musulmai a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan Sallar Idi.

Matakin da Maroko ta dauka na janye jakadanta ya zo ne bayan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana kona Alkur’anin a matsayin abin kyama.

“Ba za a kyale irin wadannan ayyukan da suka saba wa addinin Musulunci su ci gaba da faruwa ba a karkashin sunan ‘yancin fadin albarkacin baki,” a cewar wani sako da Ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Kau da ido ga irin wannan danyen aiki babban laifi ne.”

‘Yan sanda na da wuka da nama

Kona litattafai na addini “rashin mutunci ne da cutarwa”, in ji mataimakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, a bayanin da ya yi wa manema labarai.

“Duk wani abu da ka iya zama doka ba lalle bane ya zama ya na da kyau ,” in ji Vedant Patel.

Noa Omran, mai ilimin fasaha dan kimanin shekaru 32 daga birnin Stockholm, ya bayyana kona Alkur’anin a matsayin “rashin hankali”.

“Nuna kiyayya ce kawai ake yi da sunan dimokuradiyya da ‘yanci, kuma hakan ba daidai ba ne,” a cewar wata mata da ta ce mahaifiyarta ‘ta fito daga gidan Musulunci’ a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Izinin da ‘yan sandan suka bayar na kona littafin mai tsarki na zuwa ne makonni biyu bayan da wata kotun daukaka kara ta Sweden ta yi watsi da matakin da ‘yan sandan suka dauka na hana kona Kur’ani har sau biyu a Stockholm.

Firaministan Sweden Ulf Kristersson ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa ba zai yi hasashen yadda kona littafin mai tsari zai iya shafar tsarin NATO na Sweden ba.

“A hukumance haka ne amma bai dace ba,” in ji shi, ya kuma kara da cewa ‘yan sanda ne za su yanke hukunci kan hari da ake kai wa littafin Musulmai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here