Karin kudin jami’a ya jefa iyaye da dalibai cikin zullumi

0
133

Jami’ar Bayero da ke Kano ta kara kudin makaranta ga sababbi da tsofaffin dalibai masu karatun digiri na farko da na biyu.

Jami’ar ce ta bayyana haka a wata sanarwa a shafinta na Facebook dauke da bayanai kan yadda karin kudin makarantar ya shafi tsangayoyi daban-daban.

Wannan karin na zuwa ne makonni kadan bayan Gwamnatin Tarayya ta sanar da fito da tsarin ba dalibai bashin kudin karatu mara ruwa, wanda tun a lokacin aka soma hasashen cewa za a yi karin kudin makaranta a fadin kasar nan.

A cikin sanarwar da ta fitar dauke da sa hannun Mukaddashiyar Magatakardarta, Amina Umar Abdullahi, bayan kammala taron Majalisar Gudarwarta karo na 405 wanda ta ce ta gudanar a ranar Litinin, 19 ga Yuni, Jami’ar ta Bayero ta ce karin zai soma aiki ne a zangon karatu na 2022/2023.

Daliban tsangayoyin koyar da Fasaha da Addinin Musulunci da Shari’a da Ilimin Zamantakewa da Kimiyyar Gudanarwa za su rika biyan Naira 95,000 a matsayin kudin makaranta duk shekara, sa’annan sababbin dalibai a tsanagayoyin za su biya Naira 105,000.

Daliban tsangayoyin koyar da Aikin Banki da Hada-Hadar Kudi da Lissafin Kudi za su koma biyan Naira 97,000 inda sababbin dalibai kuma su biya Naira 107,000.

Dalibai daga tsangayoyin koyar da Ilimin Kwamfuta da Sadarwa da Kasa da Muhalli za su rika biyan Naira 100,000 sai kuma sabbin dalibai su biya Naira 110,000.

Dalibai a tsangayar koyar da Ilimin Albarkatun Kasa da tsangayar koyar da Tsara Taswirar Birane za su koma biyan Naira 105,000 sannan sababbin dalibai su biya Naira 115,000.

Baya ga kudin makaranta, jami’ar ta kara kudaden da ake biya na dakunan kwanan dalibai.

A cewar sanarwar, dakin dalibai maza mara gado da katifa ya koma Naira 37,590, sai kuma daki mai gado da katifa 57,590. Sai kuma dakin dalibai mata mai gado da katifa ya koma 80,090.

Sannan dakin kwanan dalibai na mata ’yan Najeriya masu digiri na biyu ya koma Naira 200,000, sai kuma na mata wadanda ba ’yan Najeriya ba ya koma 200,000.

Dakin maza ’yan Najeriya masu digiri na biyu ya koma Naira 150,180 sai kuma wadanda ba ’yan Najeriya ba 300,000.

Wannan karin na Jami’ar BUK na zuwa ne bayan Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta yi nata karin a watannin baya.

Ana fargabar sauran jami’o’in Najeriya ma za su yi irin wannan karin a zangon karatunsu na gaba.

Sai dai wani malamin jami’a ya ce wannan karin ma somin-tabi ne, domin a cewarsa, har yanzu ba a riga an sanar da cire kudin shiga makaranta da ake kira Tuition Fee ba tukuna.

Idan ba a manta ba, a bara Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta shafe kusan wata 8 tana yajin aiki, inda daga cikin bukatunta akwai ba jami’o’in ’yanci da neman karin kudaden gudanarwa, kudin da gwamnati ta ce ba za ta iya bayarwa ba.

Hakan ya sa tun a lokacin, Gwamnatin Tarayya bayan an samu maslaha, ta bayyana cewa za a samar da hanyoyin da jami’o’in za su rika samar da kudaden shigar da za su rika amfani da su wajen gudanarwa.

A lokacin, an yi ta tata-burza tsakanin ASUU da gwamnati, da kuma iyaye da dalibai, inda a lokacin iyaye da dalibai da dama suka koma bayan gwamnati, wasu kuma suke bayan ASUU.

A daya bangare, an tado da wata dadaddiyar adawa a Facebook tsakanin wani malamin jami’a, Dokta Aliyu I. Aliyu da Barista Audu Bulama Bukarti.

Dokta Aliyu ya rubuta a Facebook cewa, “Haka mambobin ASUU muka azabtar da kanmu tsawon wata takwas ba albashi saboda a yi gyara a tsarin ilimi. Har yau din nan ba a biya mu albashinmu ba.

“A lokacin da yawan yaran nan da iyayensu murna suke an aiwatar mana da tsarin ba aiki ba albashi. Kuma mun fada musu tun a baya, illar kai ASUU kasa fa su za ta fi shafa suka yi kunnen uwar shegu.

“ Yanzu mu dai sai dai mu ce Allah Ya kawo abin biyan kudin makaranta kawai,” in ji shi.

Sannan ya yada wani tsohon faifan bidiyon tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige a tattaunawarsa da tashar Channels, inda yake bayyanawa a ciki cewa, “ASUU sun ce ba za mu kara kudin makaranta ba, suna cewa idan muka kara kudin makaranta za su shiga yajin aiki.

Suna son ’yancin cin gashin kansu, su rika zaben shugabanninsu da kansu, amma kuma ba sa so su rika samar da kudi.”

A karshe ya ce za su yi duk mai yiwuwa kafin su bar gwamnati domin tabbatar da cewa jami’o’in Najeriya sun fara samar da kudaden da za su kashe.

Sai Dokta Aliyu ya sake rubuta cewa, “Yanzu sai su je wajen lauya mazaunin Ingila da sauran mazauna kasashen waje da suke ba su fatawar zagin ASUU su kawo musu mafita ai.”

Da wannan ne Barista Audu Bulama Bukarti, wanda mazaunin Ingila ne ya yi wani rubuce-rubuce masu zafi a matsayin martani, duk da Aminiya ta lura ya goge wasu daga baya.

A rubutunsa na karshe ya ce, “Yanzu dai an yi walkiya kowa ya ga ASUU a fili. ASUU ba ta taba yajin aiki don dan talaka ba.

Lokacin da ’yan kanzagin kungiyar suka kama karyar cewa suna yajin aiki ne don Malam Talaka, mun kalubalance su cewa su kawo mana misalin lokaci daya tal da ASUU ta yi yajin aiki don an kara kudin makaranta, amma suka kasa.

Saboda haka, muka ce musu a baya ASUU ba ta taba yajin aiki domin an kara kudin makaranta ba kuma a gaba ma ba za yi ba.

Don haka ba abin mamaki ba ne don ASUU ta yi tsit yanzu. Hasali ma matsa wa gwamnati da ASUU ta yi daya ne daga dalilan da suka sa ake ta wannan kare-karen.

Karin kudin makaranta zai yi matukar cutar da ’ya’yan talakawa. Amma duk da haka, gara kari da a rufe makarantun kwata-kwata kamar yadda ASUU ta saba yi.

Ai da babu gara ba dadi. Da babu gara da tsada. Game da wadanda ba za su iya biya ba kuwa, ina kira ga jami’o’i su duba yiwuwar sassauto da kudin makaranta.

Haka kuma, ya kamata jami’o’i su duba hanyoyin tallafa wa dalibai marasa karfi. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta inganta tsarin ba dalibai bashi ta yadda duk mai bukata zai samu.

Sannan ina kira ga masu hannu da shuni su tallafa wa dalibai masu karamin karfi. In sha Allah, idan lokacin rajistar BUK FUGA ya yi zan tallafa wa wani adadin dalibai da wani bangare na kudin. Ina kira ga masu dama-dama irina cewa su ma su yi haka.

Ba sai ka zama biloniya za ka iya taimakawa ba. Muna rokon Allah Ya tallafi ’yan uwanmu, Ya ba su hanyar daukar dawainiyar karatunsu ko na ’ya’yansu. Allah Ya yi mana sutura baki daya.”

A kasar wannan rubutu ne wasu suka masa ca, inda wasu suke cewa borin kunya, wasu kuma suke cewa za su kawo masa sunayen daliban da zai biya musu, sannan wasu suka yaba.

Abin da daliban BUK suke cewa

A Kano, iyaye da daliban Jami’ar Bayero ta Kano sun koka a kan karin kudin makarantar.

Aliyu Abubakar, dalibi ne a Sashin Nazarin Aikin Gona da ke jami’ar ya ce karin ya zarce yadda suka yi tsammani, kuma da dama daga cikinsu sai dai su hakura da karatun ko da kuwa suna shekarar karshe ce.

“Da farko labari muke ji, amma duk tunaninmu bai wuce karin da za a yi ba zai dara Naira 10,000 zuwa 20,000 ba.

Amma sai muka daga Naira 40,000 da muke biya a baya ya kai har Naira 101,000. To kin ga karin ya kai wajen na Naira 60,000, kuma ya sanya mutane da dama za su hakura da karatun.

Saboda wasu biya wa kansu suke, wasu kuma biya musu ake yi. Misali ni ina biya da kaina ne, da ina biya wa kaina Naira 40,000, yanzu yadda za a yi in samu wannan kudi shi ne abu mai wahala.

Gaskiya gaba daya dalibai babu wanda ya ji dadin karin. Sannan bayan kudin makarantar an kara kudin dakin kwanan dalibai, a baya Naira 15,000 muke biya yanzu ya kai Naira 57,000,” in ji shi.

Wata daliba mai suna Ummukulsum Bakoji da ke aji na uku, ta ce karin nan ba fa karamar barazana ba ce ga ilimin talaka.

Ta ce, “Kamar ni kin ga har yanzu na kasa fada wa mahaifiyata saboda ni da kanwata da za ta fara jami’a bana za ta biya wa.

Ita ce take daukar nauyinmu saboda mahaifinmu ya rasu, shi ya sa ni yanzu ban ma san yaya zan yi in fada mata wannan mummunan labarin ba.”

Ita ma A’isha Haruna Maikano da ke aji na uku a sashin ta ce ko a lokacin da ake biyan Naira 30,000 ma sai an hada da taimako suke iya biyan kudin makarantar, ballantana yanzu da ya kai Naira 100,000.

Ta ce, “Wasunmu mun sani sai da taimako suke samu su biya, ballanatana yanzu. Ni dai ina addu’ar Allah Ya dafa min in biya don na san ba zai zo da sauki ba, saboda mu uku ne muke karatu a jami’a a gidanmu.

Duk da makarantunmu daban-daban amma kin san karin ba iya BUK ba ne, sannan cikinmu akwai wadanda suke sakandare da su ma sai an biya musu kudin makaranta.

Amma dai in sha Allah muna sa ran Allah zai dafa mana mu iya biya dukkanmu.”

Wani dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD), Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa su tun a farkon shekara, aka yi musu irin wannan kari.

Ya ce, “Ban taba shan wahala wajen biyan kudin makaranta kamar a bana ba.”

Ya ce a baya lokacin da yake sabon dalibi Naira 52,000 ya biya, inda kamata ya yi a bana ya biya Naira 37,000 saboda mafi yawa daliban da suke komawa suna biyan kudi, kasa da abin da suka biya a shekarar farko.

Sai dai, maimakon haka jami’arsu a bana, ta bukaci ya biya Naira 90,000. Iyaye da sauran al’ummar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan lamarin musamman ma a kafafen sada zumunta.

Wani matashi mai suna Ahmad Salisu G-town cewa ya yi kasancewar abin da babba ya hango ko yaro ya hau rimi ba lallai ya gano shi ba, ya sa ASUU ta rika fama da gwamnati a baya don ta biya wadannan kudade, amma al’umma suka gaza fahimtarsu.

Ya ce, “Lallai Allah Ya jikan ASSU ba don sun mutu ba. Abin da suke guje wa ’yan Najeriya ke nan amma aka rika ganin laifinsu ana cewa su ne matsalar ilimi a Najeriya.

Ga shi ba a je ko’ina ba talakawa mun soma ji a jikinmu. Sai dai mu ce Allah Ya kawo mafita ta alheri.”

Shi ma Jibril Abdulkarim makamancin wannan ra’ayi gare shi, inda ya ce sai yanzu ne ya gano abin da ASUU suka yi ta kokarin nusashshe da mutane a baya amma aka gaza fahimta.

Wani matashin mai suna Isah Nuraddeen ya ce yanzu dai ta bayyana cewa janye yajin aiki da kungiyar ta yi a baya ba domin ta samun biyan bukatarta ba ce, illa damunsu da al’umma suka yi.

Ya ce, “Sun yanke hukuncin bullo da yadda za su rika samun kudin gudanar da makaranta daga jikin iyayen dalibai tunda gwammati ta gaza.

Sai dai kawai mu yi addu’ar Allah Ya hore wa iyayenmu yadda za su rika dawainiya da mu da karatunmu.

Sannan muna kira ga hukumomin makarantu su taimaka su dubi halin da talaka ke ciki a Najeriya, su sassauta mana saboda karin ya yi yawa sosai.”

Wata mahaifiyar daliba da za ta fara karatu a Jami’ar BUK, Zainab Usman ta ce ba ta ji dadin wannan kari ba, amma duk yadda za ta yi ko da za ta saka tsumma ne, sai ’ya’yanta sun yi karatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here