Wasu ma’aikata hudu sun damfari karamin bankin kasuwanci Naira miliyan 150 a Legas

0
127

A ranar Juma’a ne aka gurfanar da wasu mutum hudu a gaban kotun Majistare ta Yaba bisa zargin damfarar bankin, Think Finance Microfinance Bank na Naira miliyan 150 a unguwar FESTAC Town a jihar Legas.

Wadanda ake tuhumar sun hada da shugaban kamfanin na Risk Management, Ojimi Ayodeji, jami’in bayar da lamuni, Isaac Eddy, Joseph Setonji da Juwon Irinyemi, kuma an gurfanar da su a gaban Alkali Patrick Nwaka bisa laifuka uku na sata.

Lauyan mai shigar da kara, Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar da kamfanin ke yi, an dora su ne da alhakin bayar da lamuni ga mutane don kasuwanci, amma sai suka hada baki suka yi amfani da sunaye na bogi wajen karbar kudi daga kamfanin har Naira miliyan 150 wanda suka raba tsakaninsu ba tare sun biya ba.

Wadanda ake tuhumar sun gabatar da daidaikun mutane tare da mika musu lambobin tantance banki da sunayen asusun ajiya da kuma hotunan fasfo wadanda ba na gaskiya ba ne don karbar kudin.

Nurudeen ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne tsakanin shekarar 2019 zuwa Disamba 2022 a bankin Think Finance Microfinance Bank dake cikin garin FESTAC.

A cewar Nurudeen laifuffukan sun ci karo da juna kuma ana hukunta su a karkashin sashe na 314, 325 (1) da 287 (a) (b) (e) na dokar laifuka ta Jihar Legas, 2015.

A wani bangare na tuhume-tuhumen ya karanto cewa, “Kai, Ojimi Ayodeji, Isaac Eddy, jami’in bayar da lamuni, Joseph Setonji, Juwon Irinyemi da sauran su a yanzu, tsakanin shekarar 2019 da Disamba 2022, a bankin Think Finance Microfinance Bank, garin FESTAC, Legas, a gundumar Legas, kun hada kai a tsakanin da juna don aikata laifukan damfara kuma ta haka ne kuka aikata laifin da zai sa hukunta ku a karkashin sashe na 325 (1) na dokar laifuka ta Jihar Legas, a shekarar 2015.

“Kai, Ojimi Ayodeji, shugaban kula da kadara, Isaac Eddy, jami’in bayar da lamuni, Joseph Setonji, Juwon Irinyemi, da sauran su a yanzu, tsakanin 2019 da Disamba 2022, a bankin Think Finance Microfinance Bank, FESTAC Town, Legas, a cikin Kotun Majistare ta Legas, sun yi zamba ta ware rancen Naira miliyan 150 ga wadanda kuka samar da lambarsu ta asusus da BBN da sunan asusun ajiya da hotunan fasfo wadanda ba na gaskiya ba, wakilcin da kuka san karya ne amma kuka aikata laifin, hakan ya sanya za a hukunta ku a karkashin sashe na 314 na dokar laifuka ta Legas, da aka gabatar a Jihar a 2015.”
Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi.
Lauyan wadanda ake kara, Barista Ola, ya roki kotun da ta bayar da belinsu cikin mafi sassaucin ra’ayi.

Ba tare da adawa daga masu gabatar da kara ba, Nwaka ya amince da bayar da belinsu a kan kudi Naira miliyan 2 kowannen su tare da mutum hudu da za su tsaya musu.
Ya ce kowane wanda zai tsaya musu zai gabatar da takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku da kotu za ta tantance, sannan ta dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga Agusta, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here