Wasu na ƙyamar yin hannu da ni – Mai sana’ar yashe masai

0
179

Aikin Auwal Tukur Sheka shi ne yashe masai, inda yake amfani da duro-duro wajen kwashe ba-haya daga masan da ya cika.

Ya ce “A wannan sana’a wasu mutanen ba su yadda su sha hannu da mu, wasu kuma ba su iya cin abinci da mu.”

Auwal dai na amfani da hanya ce ta gargajiya wajen yashe masai, hanyar da aka daɗe ana amfani da ita a baya.

A yanzu yawancin waɗanda aka musu irin wannan yasa a gidajensu ba su da ƙarfi ne na ɗauko masu yasa na zamani waɗanda ke amfani da mota mai tanki da abin zuƙe ba-haya.

Auwal, wanda ke zaune a Kano ya ce yana alfahari da sana’ar tasa kasancewar da ita ya yi aure kuma yake kula da ‘ya’yansa guda tara.

Auwal da abokan sana’arsa kan karɓi naira 5,000 a kan kowane diram ɗaya na ba-haya da suka kwashe.

Auwal a bakin aiki
Bayanan hoto,Auwal a bakin aiki
Masu kwasar kashi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here