An sanya dokar hana fita a Taraba saboda rikicin kabilanci

0
135

Gwamnatin jihar Taraba ta ayyana dokar hana zirga-zirga ta tsawon sa’o’i 24 s garin Karim Lamido, shelkwatar karamar hukumar ta Karim Lamid da kewaye daga ranar Lahadin nan, 2 ga watan Yuli.

Rahotannin sun ce ayyana wannan doka ta biypo bayan sake barkewar rikicin kabilanci a wasu sassan karamar hukumar ne, inda rayuka sama da 30 suka salwanta.

Wata sanarwar da skaataaren yada labaran gwamnan jihar Yusuf Sanda ya fitar ta ce an bai wa jami’an tsaro damar tabbatar da an kiyaye wannan doka sau da kafa, tare da tanadin hukunci mai gaauni g  duk wanda ya take ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Usamn Jada ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya kai ga ayyana wannan doka, inda ya ce rundunar ta shirya tsaf domin tabbatar da doka da oda a karamar hukumar da kewaye.

A kwanan baya ne wannan karamar hukumar ta Karim Lamido ta fada cikin matsalar rikicin kabilanci, wanda ya kunno kaai sakamakon abin da ya shafi, masarauta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here