Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da kasar jagora ga sauran kasashen nahiyar Afirka.
Ya bayyana haka ne ranar Asabar a birnin Lagos lokacin da ya karbi bakuncin Umaro Sissoco Embaló, shugaban kasar Guinea-Bissau, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS.
Shugaban ya ce ya ji dadin karbar bakuncin takwaran nasa yana mai cewa sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.”
“Ina sa ran samun hadin-kai da dangantaka mai armashi da dukkan kasashen da ke yankinmu a yayin da wannan gwamnati take faman ganin ta maido da Nijeriya a matsayin jagora a Afirka,” in ji Shugaba Tinubu.
A lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Tinubu ya sha alwashin kyautata dangantaka tsakanin Nijeriya da kasashen Afirka.
Sai dai a yayin da yake bayyana cire tallafin man fetur, ya ce galibin kasashen da ke makwabtaka ne ke cin moriyarsa don haka dole ya hana yin hakan da zummar gyara tattalin arzikin kasarsa.