Yadda faston da ya musuluntar da mabiyansa 100,000 ya yi Hajjin bana

0
164

Ibrahim Richmond, wanda ya Musulunta bayan ya kasance babban limamin Kirista na sama da shekara 15 ya gudanar da aikin Hajjin bana.

Alhaji Ibrahim Richmond, wanda ya halarci tsayuwar Arfa sanye da farin Ihrami, bai san sadda ya fashe da kukan farin ciki ba, bayan isarsa Dutsen Rahama (Jabal Rahma) da ke a Filin Arfa.

Ya sauke farali ne wata uku bayan ya musulunta, ya kuma lakkana wa mabiyansa su sama da dubu 100 Kalmar Shahada a cikin cocin da yake jagoranta a kasar Afrika ta Kudu.

“Wannan ikon Allah ne, na rasa yadda zan bayyana irin farin cikin da nake cike da shi,” in ji Alhaji Ibrahim Richmond a ranar Arfa, a lokacin da yake magana game da musuluntarsa da kuma zuwansa Hajji.

“Allah Shi ne kada abin bauta wa da gaskiya, Musulunci shi ne haske da gaskiya, don haka za mu bi koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama,” in ji Alhaji Ibrahim.

Ya ce Hajjin da ya zo, wata dama ce gare shi, “Domin kasancewa a cikin ’yan uwana na Musulunci da kuma yin addu’o’i da rokon gafara Allah a gareni da sauran mutane,” a wannan sabon babi na rayuwarsa.

Ya samu yin aikin Hajjin ne karkashin kulawar Fadar Sarki Muhammad Salman Bin Abdulazeez na kasar Saudiyya.

“Na koyi darussa masu yawa a aikin Hajjin nan da muka yi, Allah Ya sa mun yi aikin Hajji karbabbe,” in ji shi bayan kammala jifa a Mina, kafin konawa zuwa Makkah.

A jawabinsa ga alhazai 4,950 daga kasashe 92 wadanda Sarki Salman ya dauki nauyinsu kafin su bar Mina bayan kammala jifa, Alhaji Ibrahim Richmond ya ce, “Kaunar da kuka nuna mini ban taba samun irinta ba a rayuwata.

“Ina rokon Allah Ya saka muku da alheri a bisa hakan da kuma abubuwan da na koya daga wurinku.

“Ina godiya ga Allah da Ya kawo mu daga kasashe daban-daban muka sauke farali, da kuma ni’imar da Ya yi mini da irin kauna da sauran abubuwa na karamci da na gani.

“Ya Allah Ka amsa addu’o’inmu, ka albarkaci rayuwarmu, Ka kara albarka ga biranen Makkah da Madina, Ka albarkaci Sarki Salman da dukkanmu da muka zo wannan ibada, da ma duk mai hannun a cikin aikin Hajji.”

Dalilin zuwana Hajji bayan na musulunta da wata 3 —Ibrahim Richmond

Ya bayyana cewa ya musulunta ne bayan da ya yi ta yin mafarkai, inda a ciki ake umartar sa da ya yi hakan

“Na fi shekara 15 a matsayin Babban Fasto inda nake jagorantar mabiya sama da 100,000, har zuwa lokacin da na yi mafarki.

“Yanzu wata uku ke nan da na karbi Kalmar Shahada a cikin cocin kuma mabiyana suka amsa tare da amincewa.

“Mun hadu da wani dan uwa Musulmi da ya fara zuwa wurinmu, inda na shaida masa cewa shi nake jira kuma na yi mafarki cewa zai zo nan,” yin aikin Hajji, in ji Alhaji Ibrahim.

Yadda Richmond ya je aikin Hajji

Anwar Yusuf daga yankin Durban na kasar Afirka ta Kudu, wanda ya ba wa Richmond da mabiyansa Kalmar Shahada, kuma suka yi aikin Hajji tare ya bayyana zuwan nasu a matsayin wata baiwa.

Ya bayyana a ranar Tsayuwar Arfa cewa “Har yanzu abin kamar mafarki nake gani, saboda ban taba tsammani ba.

“COVID-19 ya hana zuwa aikin Hajji, ya sa an rage yawan kujeru, sannan uwa uba, a bisa tsarin kasarmu, sai nan da shekara biyu zuwa uku zan iya komawa Hajji, saboda haka ban sa rai ba, ban kuma nemi gurbi ba.

“Kwatsam sai ga gayyata [daga Sarkin Saudiyya] cewa bana za mu yi aikin Hajji, har yanzu wani lokaci ji nake kamar a mafarki.”

Yadda Alhaji Richmond ya musulunta

Ya ce “A ranar 7 ga watan Afrilu ne muka fara haduwa da Sheikh Ibrahim a cocinsa, inda Allah Ya cikin rahamarSa, Ya sa na zama sila, ya karbi Kalmar Shahada, kuma tun daga lokacin muka zama abokai.

“A cikin kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ne na je yankin Amlaz, inda wani dan uwa ya shaida mini cewa akwai wani coci da mabiyansa suke yin shiga kamar Musulmi, amma idan ya nemi wasu Musulmi su je su ga abin da ake yi a cocin sai su ja baya.

“Don haka ya bukaci mu je, na amince. Da muka je, duk inda muka wuce da sallama ake gaisawa.

Coci mai alamar wata da tauraro

“A saman cocin kuma alamar wata da tauraro aka sanya (ba Kuros ba).

“Da muka shiga sai muka samu gaisawa da manyan fastoci, har wani mai suna Juma wanda shi ma yanzu ya musulunta ya tambaye mu, ‘me ya kawo ku?’

“Na ce, mun ga alamar wata da tauraro ne a saman ginin, mun dauka masallaci ne, shi ne muka shigo [yin Sallah].

“Sai suka ce, ai su ba Musulmi ba ne, sai na ce to me kuke bauta wa? Juma ya ce Ubangiji suke bauta wa. Amma da na bukaci ya yi min bayanin abin da suke bauta wa, sai ya ce sai dai ya haɗa ni da fastonsu zai fi iya yi mini bayani, amma sai dai mu dawo zuwa anjima.

“A hanyarmu ta fita duk waɗanda muka hadu da su a harabar katafaren cocin, sai sun gaishe mu sun ba mu hannu cikin sakin fuska kamar sun taba sanin mu.

“Muna gab da mu fita ne muka hadu da wani dattijo (Alhaji Ibrahim), inda ya tare mu cikin murmushi, ya bude hannuwansa zai rungume ni.

“Da ganin yadda mutane ke kauce masa a hanyar, sai na fahimci cewa wani babba ne a cocin, saboda haka sai na matsa kusa muka rungume juna, a nan ne ya yi mun radar cewa ‘na dade ina jiran ka’.

“Da jin haka sai na fara tunani, na ce masa a ina za mu tattauna, ya bukaci mu shiga ciki, amma abin ya gagara saboda yawan mutane a harabar.

“Sai ya ce mu fita waje, da muka fara magana sai ya shaida mini cewa, kimanin sati uku da suka wuce ya yi mafarki cewa zan zo.

“Da jin haka sai na rasa me zan yi, amma na bukaci ya ba mu lokaci zan dawo bayan awa biyu.”

Fasto ya ba wa mabiyansa Kalmar Shahada

“Lokacin Sallar Tarawih sai muka tattauna da wasu abokaina muka dawo mu uku.

“Da dawowar sai muka ga sun kara girmama mu — ban taba samun girmamawa haka ba — aka ba mu kujera a gaba a kusa da shi,” in ji Anwar.

Ya shaida wa kafar yada labarai ta kasar Saudiyya cewa bayan shigar su coci, faston ne ya mike ya yi rika yi wa mabiyansa jawabi da wa’azi a kan Musulunci, “saboda haka shi ya yi mana aikin da’awa, mu Kalmar Shahada kawai muka ba su.

“Mutum kimanin 600 ne suka karbi Shahada da farko, amma da za mu tafi sai ya ce mana ‘ku dawo anjima’, amma muka ce sai baya Tarawih.

“Ya ce duk lokacin da muka gama mu dawo, da muka dawo a cikin daren kuma, muka samu ginin cocin da harabarsa sun cika da jama’a babu masa tsinke.

“Da muka shiga, sai ya kara yin jawabi, na karanta Kalmar Shahada, yana yi, daukacin jama’ar da ke cocin suna amsa wa — saboda haka ana iya cewa shi ya ba su Kalmar Shahada — dadin abin ya wuce misali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here