‘Yan bindiga sun kashe wani fasto tare da garkuwa da mambobinsa

0
99

‘Yan bindiga sun kutsa kai cikin wata mujami’a, inda suka kashe faston cocin tare da yin awon gaba da wasu mabobinsa a jihar Ogun.

Lamarin ya auku ne a cocin Redeemed Christian Church a garin Abule-Ori dake karamar hukumar Obafemi Owode da  misalin karfe 12 na  daren jiya Asabar, 1 ga watan Yulin nan.

Kwamandan rundunar sa kai ta So-Safe Corps, a jihar,  Soji Ganzallo,  ya tabbatar da aukuwar lamarin da safiyar Lahadin nan, kuma ya ce jami’ansa sun ceto manbobin cocin 7, tare da kashe daya daga cikin ‘yan bindigar.

Ganzallo ya ce jim kadan bayan aukuwar lamarin ne aka hori jami’ansa su farauto wadanda suka yi aika-aikar, tare da ceto mutanen da suka kama ba tare da kawarzane ba, inda su kuma cikin ikon Allah suka aiwatar da umurnin.

Ba wannan ne karo na farko da ‘yan bindiga ke cin zarafin al’umma a wannan jiha ta Ogun ba, inda ko a farkon watan Yuni sai da suka yi awon gaba da wata mata a wata mashaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here