Ghana za ta soma kama dabbobin da ke gararamba da cin tarar masu su

0
119

Sashen kula da tsaftar muhalli na Karamar Hukumar Nkwanta ta Kudu da ke kasar Ghana na shirin soma atisayen daure dabbobin gida da ake barinsu sakaka suna yawo.

Jami’ar kula da tsaftar muhalli ta Karamar Hukumar Nkwanta ta Kudu, Madam Cynthia Sekyere ce ta bayyana hakan a yayin zantawarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Ghana kan shirin atisayen da sashen da ta ke jagoranta zai gudanar cikin watan Yuli.

Ta ce yin hakan ya zama wajibi a daidai wannan lokaci idan aka yi la’akari da yawan korafe-korafe da aka yi ta samu daga al’umma kan yadda daddobin da ake barinsu kara zube ke addaba tare da lalata muhallin al’ummomin yankin.

Ta ce an kafa wani kwamiti da zai sa ido kan wannan aiki wanda ya kunshi mambobin majalisa da wasu kwamitoci da ke karamar hukumar domin gudanar da atisayen.

“Biyo bayan korafe-korafen da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya samu daga jama’a kan irin barnar da dabbobi kan yi a unguwanni da tituna daban-daban, har ma da yin bahaya a wuraren da jama’a ke zama, ya sa mu daukar wannan mataki ”a cewar Madam Cynthia.

Jami’ar ta ce, yunkurin zai taimaka wajen takaita gararambar da dabbobin gida kamar awaki da tumaki da karnuka ke yi tare da taimakawa wajen hana daukar cututtukan da ake samu daga jikin dabbobi (zoonotic) da kuma dakatar da barna da suke kan gonaki, lambuna da kuma kiyaye afkuwar hadurra a kan hanyoyi daban-daban da dabbobi ke janyowa.

Madam Sekyere ta kuma kara da cewa za a ci tarar duk wani da ya mallaki wata dabba da aka kamata da wannan laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here