Drogba ya soma yaki da masu zaluntar ‘yan kwallon Afirka

0
154

Tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya sha alwashin magance matsalar nan ta wakilai ko ejent na bogi da suka dade suna damfarar ‘yan kwallon kafar Afirka.

Wani bincike da kungiyar ‘yan kwallon kafar duniya mai suna Fifpro ta yi, ya nuna yadda wakilai na bogi suke yaudarar matasan ‘yan kwallon Afirka da ba su dade a harkar ba, inda suke yi musu alkawarin kai su Turai da wasu nahiyoyi domin murza kwallon kafa.

“Fatan wadannan matasan ‘yan kwallon kafa yana komawa abin takaici” bayan an damfare su, a cewar Drogba.

Ya kara da cewa daga yanzu gidauniyarsa za ta hada gwiwa da FIFPRO da Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) domin fadakarwa tare da taimaka wa ‘yan wasa don kada su fada hannun wadannan ‘yan damfara.

“Don Allah, Ina so ku ji wannan,” a cewar tsohon dan wasan na kasar Ivory Coast a wani bidiyo da ya nada domin matasan ‘yan wasan. “Ku yi hattara kan muanen da za ku amince da su. Kada ku taba amincewa da mutanen da ke son karbar kudinku.”

Binciken da FIFPRO ta yi kan ‘yan wasa 263 daga kasashen Afirka bakwai ya nuna cewa wakilai na bogi sun tuntubi kashi 70 daga cikinsu inda suka yi musu alkawarin taimaka musu don sauya kungiyar kwallon kafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here