Gwamnatin Kano ta fara bincike akan Ganduje

0
150

Hukumar Karbar Koke da Yaki da Cin Hancin da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta kaddamar da fara bincike akan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin karbar dala da wani faifan bidiyo ya nuna yana karba.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana hakan a lokacin da ya tabbatar da cafke tsohon kwamishinan jihar, Injiniya Idris Wada Saleh akan zargin badakalar dala biliyan daya.

Muhuyi wanda ya sanar da hakan a taron manema labarai a jiya Talata ya ce a yanzu haka hukumar ta kaddamar da fara bincike wanda kuma ta karbi rahoton binciken faifan bidiyon karbar dalar da ake zargin Ganduje.

A wani shirin tattaunawa da gidan talabijin na Trust, Muhyi ya lashi Takobin bude faifan bidiyon da suka nuna Ganduje yana karbar daloli yana zuba wasu a cikin aljihunsa a matsayin cin hanci daga wajen wani dan kwangila, wanda Ganduje ya karyata hakan.

A cewarsa, “babu wata kotu da ta taka mana birki kan wannan matakan da muke dauka.”

Shugaban ya kara da cewa, hukumar ta kuma rubutawa EFCC wasikar neman yin hadaka don yin binciken tare da ganin an hukunta Ganduje.

A cewarsa, ganin cewa hukumar ba ta riga ta samu wata amsa daga wajen EFCC kan wasikar da ta aika mata ba, PCACC za ta gudanar da nata binciken ta hanyar janyo sauran hukomomi cikin binciken.

Da yake yin tsokaci akan zargin badakalar kama tsohon kwamishinan kan almundahanar Naira biliyan daya, shugaban ya ce tsohon kwamishinan ya yi hakan ne, da sunan yin gyaran wasu hanyoyin jihar a cikin mako daya da gwaman jihar ke sihirin sauka daga mulki.

Ya ce, an kuma kama Manajin Darakta na hukumar gyaran hanyoyi na jihar (KARMA) tare da babban sakataren hukumar BPP na jihar, Mustapha Madaki Huguma da Daraktan kudi da kuma Daraktan sashen bincike da tsare-tsare na jihar a ranar Litinin.

Ya ce, kudin da ake magana akai an fitar da su an kuma turawa kamfanonin an fitar da su ne a ranar 25 ga watan Afirilu.

A wata sabuwa kuwa, kotun majistare a jihar Kano, ta bayar da umarnin ajiye tsohon kwamishinan har zuwa kwanaki 12 kafin a kammala bincike.

An kai shi gaban kotu ne a ranar Talata kan tuhuma biyu da suka hada sauya bayanai da kuma yin cuta.

Lauya mai gabatar da kara, Salisu Tahir kuma Mataimakin Darakta a hukumar PCACC ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhumar a 2023 ya fitar da kudin ga kamfanin Arafat Construction da kamfanin No Stone Construction da kuma ga kamfanin Multi Resources don gyran hanyoyi 30 a cikin birnin Kano wanda kuma ba a gudanar da aikin ba.

Ya kuma bukaci da a kai ajiyar wanda kotun ke tuhuma na kwana 14, sai dai wanda ake tuhumar bai amsa laifinsa ba.

Mustapha Idris, wanda yake tsayawa wanda ake tuhuma ya shawarci kotun da ta yi amfani da sashe na 35 da na 6 na kundin tsarin mulkin Nijeriya don a bayar da belinsa.

Amma a hukuncin da alkalin kotun majistaren mai shari’a Tijjani Sale-Minjibir ya yanke, ya bayar da umarnin a ajiye shi har zuwa kwanaki 12 tare da ba shi kular da ta kamata.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 14 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here