APC ta shawarci Ganduje kada ya amsa gayyata kan bidiyon dala

0
157

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aika takardar gayyata ga tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kan ‘bidiyon dala‘.

Wata sanarwa da hukumar mai taken (KPCACC) ta fitar, na cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake karɓar damin daloli daga hannun wasu ‘yan kwangila yana zubawa a aljihu.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafe, Muhyi Magaji Rimin Gado yana cewa: “Na sa hannu a kan wata wasiƙa don gayyatar shi, ya zo a yi masa tambayoyi a hukumar cikin makon gobe. Saboda abin da doka ta ce kenan kuma za mu bayar da ɗumbin damammaki don ya kare kansa”.

Sai dai, Mallam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano kuma makusancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu ba su samu takardar gayyatar da ake cewa hukumar ta aika wa tsohon gwamnan ba.

Kuma dangane da sahihancin bidiyon da hukumar Muhyi take iƙirari, Muhd Garba ya ce ba za su ce uffan a kan wannan batu ba, don kuwa magana ce da take gaban kotu.

Umar Abdullahi Ganduje dai ya sha musanta zargin, inda ya riƙa iƙirarin cewa abokan adawa ne suka shirya maƙarƙashiya da nufin hana masa damar shiga zaɓen 2019.

Mallam Muhammad Garba dai ya yi zargin cewa gayyatar da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta yi wa Ganduje, ba komai ba ne face siyasa. Ya yi iƙirarin cewa abokan adawar Ganduje ne kawai ke yunƙurin ganin sun wargaza aniyar ba shi wani muƙami kamar na minista a gwamnatin tarayya. 

“Abin mamaki ne, bai kamata idan muna aiki, mu yarda a dinga amfani da mu domin a cimma wasu abubuwa da ‘yan siyasa ke son cimmawa ba”. 

Ya ƙara da cewa ba daidai ba ne a dinga amfani da mutane don ganin an kassara wani mutum, an kai shi ƙasa, tare da cin mutuncinsa.

Ya yi iƙirarin cewa maganar ta zama ta siyasa.

Gayyatar dai na zuwa ne kwana 38, bayan Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa mulkin Kano ga gwamnatin Kwankwasiyya , a ƙarshen wa’adinsa na biyu, wanda ya fara daga 2015 zuwa 2023.

Tsohon kwamishinan Ganduje dai ya ce matakin, wani yunƙuri ne kawai na daƙile duk wani namijin ƙoƙari da tsohon gwamnan ya yi a Kano. “A ci mutuncinsa, kuma ina ganin wannan ba daidai ba ne.” 

Ya ce ya tuntuɓi Ganduje bayan samun wannan labari, inda ya tabbatar masa cewa har zuwa lokacin da yake magana da BBC (Alhamis da rana) ba a ba shi wata takardar gayyata ba.

masaniyar cewa jam’iyyar APC reshen Kano ta shawarci tsohon gwamnan kada ya amsa gayyatar hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano. 

Ya ce jam’iyyarsu ce ta fitar da wannan sanarwa. 

Sai dai ya ce duk da haka, Ganduje zai tuntuɓi lauyoyinsa domin jin irin shawarwarin da su ma za su ba shi game da wannan gayyata. 

“Saboda na san wannan magana ta bidiyo da ake zance a kai, magana ce da take gaban babbar kotun Najeriya da ke Abuja. Kuma ni a ƙaramin sanina, in dai magana tana gaban kotu, bai kamata a ce an sake tado ta ba,” in ji Muhammed Garba.

Ya ce idan lauyoyinsa sun ba shi shawara, sun ga dacewar ya je, to me zai hana shi zuwa? 

Idan kuma suka ce kada ya je saboda dalilan da suka ba shi, in ji Mallam Garba, sannan ga umarnin da jam’iyyar APC ta ba shi, saboda haka wannan abin da Ganduje ya kamata a ce ya tsaya ya yi duba ne a kansu. 

Tsohon kwamishinan ya ce saboda ba abu ne, nasa shi kaɗai ba. “Abin da ya shafe shi, ya shafi dukkan jam’iyyar APC, saboda an mayar da batun siyasa”.

Ita dai jam’iyyar APC a cikin sanarwar da shugabanta na Kano Abdullahi Abbas da sakataren jam’iyyar, Zakari Sarina suka sanya wa hannu, ta ce jam’iyyar NNPP ta sake dawo da “batun da aka tsiro da shi saboda dalilai na siyasa game da bidiyon dala wanda ke gaban kotu da wata muguwar maƙarƙashiya don zubar da mutuncin tsohon gwamnan”.

Ta ce ‘yan hana ruwa gudu ne suka shiga wannan yunƙuri na ɓata suna da nufin shiga tsakanin Bola Ahmed Tinubu da Ganduje, wanda sanarwar ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin babban aminin shugaban ƙasar a arewacin Najeriya.

APC ta ce an yi amfani da irin wannan salo don lalata damar Ganduje ta sake neman tikitin jam’iyyar don sake tsayawa takarar gwamna a 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here