Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bayan wata 18 a gidan yari

0
158

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta bayar da belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Abba Kyari.

Kyari dai ya kasance a tsare tun lokacin da aka kama shi a shekara ta 2022.

Hukumar Han sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta gurfanar da shi kan zarginsa da hannu a wata badakalar Hodar Iblis da nuyinta ya kai kilogiram 25.

Daga bisani ne aka kama shi sanna aka gurfanar da shi a gaban kotu, wacce kuma ta bayar da umarnin garkame shi a kurkukun kuje da ke Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here