Masaurata ta Dakatar da Marafan yamman Zazzau

0
236

A zaman ranar Litinin, 3 ga Watan Yuli, 2023, Majalisan Masarautan Zazzau ta duba gami da nazari bisa koken al’ummar unguwar Magajiya dake cikin Birnin Zariya wanda suka gabatar a gabanta.

A sakamakon haka, Majalisan Masarautan Zazzau ta amince cikin gaggawa da dakatar da alhaji Mustafa Adamu Ubaidu Marafan Yamman Zazzau daga wannan sarauta har sai abin da hali ya yi.

Shi dai Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, Majalisan ta same shi da laifin zartas da Hukunci da Hañnunshi ne, ta wajen hukunta wani saurayi Yusuf Yahaya (Sabo) mazaunin wannan unguwa ta Magajiya wanda a bisa dokokin shari’a da na kasa bai da izinin yi ko daukan haka.

Da kaukausar murya, a bisa ga wannan dakatarwa ga Marafan Yamman Zazzau, Majalisan Masarautan Zazzau tana jawo hankalin dukkanin hakimai da dagatai da sauran masu rike da sarautu cewan kaman yadda ba ta amince da kowane irin rashin da’a da tarbiyya a cikin al’umma ba, haka nan kuma ba ta amince da su rinka daukan doka a hannunsu ba.

Majalisan Masarautan Zazzau tana kara tunatar da duk masu rike da Sarautu a Masarautan Zazzau da su kiyaye cewan ba za ta lamunce da cin zarafi ko tozarta kowane irin jinsi na al’umma ba. Tana kuma kara jawo hankalin da a rinka mika wadanda ake tuhuma bisa laifuka ga mahukunta.

Daga karshe, Majalisan Masarautan Zazzau tana kara tabbatar ma al’umma cewan a kowane lokaci a shirye take domin daukan mataki mai tsanani ga duk wanda ya saba dokokin da shari’a ta shimfida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here