Mutanen da suka tsere wa rikicin Taraba na cikin tsananin buƙatar agaji

0
175

Yayin da rahotanni ke cewa ana ƙara samun nutsuwa, bayan rikicin ƙabilanci na tsawon kwanaki a jihar Taraba, ɗumbin mutane ne musamman waɗanda suka tsere wa gidajensu, ko aka kona musu suka shiga mawuyacin hali.

Rikicin ya faru ne tsakanin ‘yan kabikar Karimjo da Wurkun, sanadin taƙaddamar sarauta.

Hon Abdullahi Mohammed, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin ya faɗa wa BBC cewa cikin kwana biyun nan rikicin ya lafa, saboda matakan da gwamnati da jami’an tsaro suka ɗauka, amma mutane na cikin tashin hankali.

Ya ce ”Ana cikin mawuyacin hali, musamman waɗanda aka ƙona wa gidaje, mata da yara sun bar gidajensu, ga shi kuma damuna ce, abin da ya sa lamarin ya munana, don kuwa babu inda za su je, su zauna”

Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda suka gudu, suna zaune ne a makarantu, yayin da wasu kuma ke tare da ‘yan’uwansu.

Hon Abdullahi Muhammad, ya ce akwai buƙatar kai agajin gaggawa ga irin waɗannan mutane da wuri, musamman na abinci da tufafi da kuma mayafai.

Yadda rikicin ya samo asali

Ƙabilun Wurkum da Karimjo din da ke karamar hukumar sun yi artabu da juna ne kan nadin sarautar gargajiya a yankin, har ta kai ga mahukunta sanya dokar hana fita a yankin.

Rikicin ya barke ne bayan da aka bai wa Alhaji Abubakar Haruna sandar girma ta gadon mahaifinsa wanda ya yi mulkin Wurkum na tsawon shekara 47 a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce an kona kauyuka shida tare da kona mutane biyu a daren Asabar din da ta gabata.

Baya ga haka kuma an ƙona dabbobi da dama a rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here