Yadda kona Alƙur’ani ya yamutsa Sweden

0
165

Ƙona Alƙur’ani mai girma ya jefa ƙasar Sweden cikin ruɗani game da ƴancin faɗin albarkacin baki da kuma kare haƙƙin addinin marasa rinjaye.

Karon battar dake tsakanin manufofin biyu ta kuma jawo tarnaƙi ga yunƙurin Sweden na shiga ƙungiyar ƙawancen tsaro ta ƙasasashen arewacin Tekun Atalantika (NATO).

Sweden dai ta matsu da ta shiga NATO sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine amma bisa ƙa’ida ƙungiyar ba ta karɓar wata sabuwar ƙasa sai duk ƙasashen dake cikinta sun amince.

Daga cikin ƙasashen dake NATO kuma akwai Turkey wacce ta ƙi amincewa da shigar Sweden saboda zanga-zangar adawa da Musulunci da ake gudanarwa a ƙasar.

Ƙona Alƙur’ani ranar Sallah

A makon jiya ne dai  wani Kirista ɗan asalin Iraq ya ƙona littafin Alƙur’ani mai girma a ƙofar wani masallaci dake Stockholm, babban birnin Sweden a ranar Sallah Babba.

Shugaban ƴan sanda na yankin Helsingborg ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa “a Sweden, muna da ƴancin faɗin albarkacin baki. Muna kuma girmama mutanen dake da ra’ayi mabambanci, sannan ba ma son abin da zai ɓata musu rai. Don haka lamarin na buƙatar nazari.”

A farkon shekarar nan dai ƴan sandan Stockholm sun yi ƙoƙarin hana ƙona Alƙur’anin amma kotu ta ce dokokin Sweden sun amince da yin hakan.

Bisa la’akari da wannan hukuncin ne, ƴan sanda su ka bada dama a makon jiya wani Kirista ɗan Iraq ya ƙona Alƙur’ani mai girma a ƙofar masallaci ranar Sallah Babba.

Musulmi sun Koka

Jagororin Musulmi a Sweden sun yi tur da wannan aiki amma martani mafi zafi ya fito ne daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Masu zanga-zanga sun afkawa Ofiishin Jakadancin Sweden dake Baghdad. Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) ta soki hukumomin Sweden da suka bari aka yi.

Iran ta dakatar da tura sabon jakada zuwa Stockholm yayin da Pakistan ta buƙaci Majalisar Kare Haƙƙin Bil Adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya zama na musamman akan batun.

Ba Musulmi kaɗai ba, hatta Fafaroma Francis ya koka da lamarin.

Gwamnatin Sweden ta yi Suka

A nata ɓangaren, gwamnatin Sweden ta ce ta na “tsananin adawa da ayyukan nuna ƙiyayya ga Musulunci da wasu mutane ke aikatawa a Sweden” kuma ta ce “hakan bai dace da ra’ayin Gwamnatin Sweden ba.”

Hakan ya jawo ƴan gwagwarmaya a ƙasar suka yi ta sukan gwamnati inda suka tuhume da rashin kare haƙƙin faɗin albarkacin baki.

Fitaccen mai rajin kare haƙƙin faɗin albarkacin baki a Sweden Nils Funcke ya  shaidawa gidan talabijin na gwamnatin ƙasar, SVT cewa, “ba daidai ba ne ko kaɗan a cewa gwamnati na sukar wani mutum da ya aikata abinda bai saɓawa doka ba, illa dai kawai ya yi amfani da haƙƙin da tsarin mulki ya tabbatar masa na faɗin albarkacin bakinsa.

Makomar Denmark

Sweden dai ta na fargabar kar ta tsinci kanta a irin halin da Denmark ta shiga a 2006 bayan da wata mujalla ta wallafa hotunan cin zarafa da ta danganta su da Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A lokacin an ƙona ofisoshin jakadancin Denmark yayin da masu zanen suka fuskanci barazanar kisa daga masu kishin Musulunci.

Duk ƙoƙarin da jami’an Denmark suka yi a lokacin na bayyana cewa haƙƙin faɗin albarkacin baki ya dace da doka basu gamsar da ƙasashen Musulmi ba.

A binciki Rasha

Sai dai Hukumar Tsaro ta Sweden na zargin da hannun Rasha cikin wanann shiri na ƙona Alƙur’ani a makon da jami’an ƙasar za su tattauna da takwarorinsu na Turkey game da buƙatar shiga ƙawancen NATO.

Kakakin hukumar Adam Samara ya ce “Hukumar Tsaron Sweden na sane da yadda ƙasashe irin su Rasha ke juya  akalar wasu mutane daga bayan fage domin kawo ruɗani a ƙasar Sweden.”

Ƙasashen Sweden da Finland, waɗanda a da ƴan-ba-ruwana ne sun nemi shiga NATO ne bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a bara.

Kuma Rasha ta gargaɗe su da cewa za ta mayar da martani da “matakan siyasa da na soji.”

A watan Afrilu Finland ta shiga NATO, amma Turkey da Hungary sun ƙi amincewa da shigar Sweden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here